Sabuwar Takaddama Ta Barke a APC Ta Jihar Edo, Bayanai Sun Fito

Sabuwar Takaddama Ta Barke a APC Ta Jihar Edo, Bayanai Sun Fito

  • Jam'iyyar APC reshen Edo ta sake shiga rikici yayin da aka wayi gari masu ruwa da tsaki sun sa kafar wando ɗaya da shugaba na Owan ta Gabas
  • Sun zargi shugaban kwamitin kamfen Tinubu/Shettima da Oshiomhole da yin sama da faɗi da wasu kuɗaɗe
  • Tawagar masu ruwa da tsakin sun rubuta wasiƙar korafi zuwa shugaban jam'iyya na jiha

Edo - Sabuwar taƙaddama ta barke a jam'iyyar All Progressive Congress (APC) reshen jihar Edo kan babban zaben shugaban kasa wanda aka kammala a 2023.

Rigimar ta kunno kai inuwar APC ne kan kuɗaɗen da aka ware wa zaben shugaban ƙaaa da yan majalisun jiha wanda ya gudana ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.

APC da Adamu.
Sabuwar Takaddama Ta Barke a APC Ta Jihar Edo, Bayanai Sun Fito Hoto: APC, Abdullahi Adamu
Asali: Twitter

Rahoton jaridar Tribune ya tattaro cewa sabon rikicin ya taso ne daga yankin ƙaramar hukumar Owan ta Gabas, a shiyyar arewacin jihar Edo.

Kara karanta wannan

Gwamnan Jihar Taraba Ya Bayyana Gaskiya Dangane Da Batun Fitar Da N2bn a Asusun Jihar Domin Siyo Motocin Kece Raini

Me ya hawo sabon rikici a APC da mazabar Oshiomhole?

Wasu mambobin APC karkashin kungiyar masu ruwa da tsaki sun fara haɗa kai wuri ɗaya da nufin sa ƙafar wando ɗaya da Abdulganiyu Lawani, daraktan kwamitin kamfen Tinubu/Shettima, Adams Oshiomhole a arewacin Edo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Waɗanda suka ɗaura damarar wannan fafutuka suna zargin Lawani da manyan laifuka biyu, karkatar da kudaden da aka ware da kuma saɓa alkawurra a jam'iyya.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa hakan na kunshe a wata wasiƙar korafi da suka aike wa shugaban APC na jihar Edo, David Imuse, wacce wani Abdullahi Isa, ya marawa baya, daga baya ya ce bai san komai ba.

A takaice sun zayyana tuhume-tuhume 9 a kan Lawani kuma sun bukaci jam'iyya reshen jiha ta gudanar da bincike, idan har yana da laifi ta ɗauki matakin gaggawa a kansa.

Kara karanta wannan

Manyan Arewa Daga Jihohi 19 Sun Gana a Kaduna, Sun Aike da Sako Ga Tinubu Kan Majalisa Ta 10

Masu ruwa da tsakin sun nemi jam'iyya ta tilastawa Lawani ya dawo da kuɗaɗen da ya yi sama da faɗi da su. Sun kuma nemi APC ta sahale musu su kai ƙara Kotu.

Ana zargin Lawani da sauya akalar miliyoyin kudin da aka tara domin haɗa kan magoya baya da kayayyaki a lokacin kamfen Bola Tinubu da Adams Oshimhole.

Kalu zai janye daga takara - Adamu Garba

A wani labarin kuma Babban Jigon APC Ya Faɗi Ɗan Takarar da Ba Zai Zama Shugaban Majalisar Dattawa Ta 10.

Adamu Garba, ya ce Kalu ba zai iya cin zaben shugaban majalisa ba saboda jam'iyya ba ta taɓuka komai ba a Kudu maso Gabas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel