Shugaban Majalisa: Sanatoci 18 Sun Botsarewa APC, An Fito da ‘Yan Takara Dabam

Shugaban Majalisa: Sanatoci 18 Sun Botsarewa APC, An Fito da ‘Yan Takara Dabam

  • Ba dole jam’iyyar APC ta samu yadda ta ke so cikin sauki a zaben shugabannin majalisar tarayya ba
  • Wasu ‘yan majalisa ba za su zabi Godswill Akpabio da Barau Jibrin ba, su na goyon bayan wasu dabam
  • Akwai Sanatocin Arewa da suke ja da jam’iyya, watakila su bi bayan Orji Uzor Kalu da Abdulaziz Yari

Abuja - Yunkurin jam’iyyar APC na tsaida Godswill Akpabio da Barau Jibrin a matsayin shugabannin majalisar dattawa ya na fuskantar matsala.

Rahoto ya fito daga Sun cewa akwai zababbun Sanatocin da sun sha alwashin yakar Godswill Akpabio da Barau Jibrin su na goyon bayan wasu dabam.

A maimakon su goyi bayan zabin jam’iyya mai-ci, zababbun ‘yan majalisar za su mara baya ga Sanata Orji Uzor Kalu da Abdulaziz Yari a zaben bana.

Shugaban Majalisa
Zaman Majalisar Dattawa Hoto: @NgrSenate
Asali: Facebook

Godswill Akpabio zai karbu?

Kara karanta wannan

Akpabio/Barau: Abubuwan da Ya Dace a Sani Game da Sababbin Shugabannin Sanatoci

Wani Sanata daga jihar Arewa maso yamma ya soki matsayar Bola Tinubu, ya zarge shi da takalar fada domin a cewarsa Godswill Akpabio bai da farin jini.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sanatan ya ce ana zargin Akpabio da hannu wajen ganin bayan Sanatan jiharsa, Bassey Albert da Sanata Peter Nwaoboshi saboda manufarsa ta siyasa.

Haka zalika wani fitaccen Sanata daga Arewa maso gabas ya shaidawa jaridar cewa za su fito da ‘dan takaransu dabam da wanda jam’iyyar APC ta tsaida.

Tikitin Uzor Kalu/Abdulaziz Yari

‘Dan majalisar ya ce sun gamsu da tikitin Yari da Orji Kalu, don haka su za su kadawa kuri’arsu.

Haka zalika wasu zababbun Sanatoci daga jihohin Arewa maso tsakiya ba su tare da APC, su na ganin babu adalci a yadda jam’iyya mai mulki tayi rabonta.

‘Yan majalisa 18 masu jiran gado sun aika wasika ga shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu, sun ce sam ba za su goyi bayan kason da aka yi ba.

Kara karanta wannan

Har An Soma Zargin Tinubu da Rashin Adalci Tun Kafin Hawa Mulki Kan Takarar Majalisa

A cikinsu akwai Mohammed Sani Musa, Ashiru Oyelola Yisa, Sadiq Umar Suleiman, Mustapha Saliu da Isah Jibrin daga Jihohin Neja, Kwara da kuma Kogi.

Matsayar Hon. Kawu Sumaila

Rahoton ya kara da cewa zababben Sanata, Abdulrahman Kawu Sumaila ya ce wasu sun kai Bola Tinubu sun baro shi a game da shugabancin majalisar dattawa.

Sumaila wanda zai wakilci Kano ta Kudu a NNPP ya gargadi Tinubu ya guji karfa-karfa, ya ce APC ba ta isa ta fada masa wanene zai zama shugabansa ba.

Majalisar wakilan tarayya

A baya rahoto ya fito cewa akwai ‘yan majalisar APC da-dama da suke burin hana Tajudeen Abbas zama sabon shugaban majalisar wakilan tarayya a 2023.

Ahmed Wase, Aliyu Betara, Sada Soli, Ado Doguwa da Sani Jaji duk su na takara, sannan ‘Yan LP 31 da za su je majalisar tarayya sun yarda su hada-kansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel