Jigo Ya Tona Tsohon Gwamna da Ya Ci Amanar Tinubu, Ya Goyi Bayan Atiku a Asirce

Jigo Ya Tona Tsohon Gwamna da Ya Ci Amanar Tinubu, Ya Goyi Bayan Atiku a Asirce

  • Blessing Agbomhere ya ce Rotimi Amaechi ya ci amanar jam’iyyarsa ta APC a zaben shugaban kasa
  • Sakataren gudanarwar APC na Kudu maso kudu ya ce tsohon Ministan da yaransa sun goyi bayan PDP
  • Agbomhere yana ikirarin sun yi waje da Victor Giadom, shi kuma ya dare kan kujerarsa a jam’iyya

Abuja – Sakataren gudanarwa na APC a Kudu maso kudu, Blessing Agbomhere ya zargi Rotimi Amaechi da kitsawa jam’iyya mai ci makarkashiya.

A wani dogon rahoto da aka samu a Punch, an ji Blessing Agbomhere ya na tuhumar tsohon Ministan sufuri da laifin yakar Bola Tinubu a zaben 2023.

‘Dan siyasar ya ce tsohon Gwamnan na jihar Ribas da mutanensa sun yi kutun-kutun domin ganin Bola Tinubu bai kai labari ba a zaben shugaban Najeriya.

A cewarsa, Victor Giadom ba zai cigaba da rike mukaminsa na shugaban shiyyar Kudu maso kudu na jam’iyya ba domin shi ya karbe kujerar da yake kai.

Kara karanta wannan

Atiku ne ya lashe zabe: PDP ta caccaki ministan Buhari, ta tono barnar APC

APC ta sauke Giadom da Ita Udosen?

Yayin da Agbomhere ya ce ya canji Giadom, ya kuma nuna an yi waje da Ita Udosen daga APC.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Rahoton ya ce jagororin jam’iyyar APC sun fatattaki Giadom ne a ranar Lahadi bayan shugabannin shiyyoyi biyar na APC sun nuna ba su tare da shugabannin.

'Yan APC
Yakin zaben APC Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Uwar jam'iyya tayi martani

Haka ya jawo Sakataren yada labaran APC, Felix Morka ya fitar da jawabi da ya zama raddi, yana mai cewa Agbomhere ba su da hurumin tsige shugabanni.

Da yake maida wani martanin a Abuja, Mista Agbomhere ya soki jawabin Felix Morka, ya ce Amechi da Giadom ba su taimaki jam’iyya a zaben bana ba.

"Victor Giadom bai kawo jama’a domin a taimakawa jam’iyyarmu ta APC a babban zabe ba. Bai goyi bayan ‘dan takaranmu (Tinubu) ba.

Kara karanta wannan

2023: Za a yi zaben gwamna a Kogi a watan Nuwamba, Tinubu ya fadi dan takararsa

Bola Tinubu da Kashim Shettima sun zauna da yaransu domin sun san Rotimi Amaechi ya shiga zaben tsaida gwani, bai yi nasara ba.
Amaechi da Giadom ba su yi wa APC aiki ba. Sun fito karara su na kiran taro a Kudu maso kudu, su na kira ga mutane su zabi Atiku Abubakar.
Mu na ganin wannan cin amana ne saboda ganin irin duk abubuwan da APC tayi wa Amaechi.

- Blessing Agbomhere

Kira zuwa ga gwamnatin Tinubu

A rahoton da aka fitar a safiyar Talata, an ji labari Shugaban Najeriya mai haramar barin gado ya ba Bola Tinubu shawarar ya kula da ‘yan kwadago.

Muhammadu Buhari yana so ma’aikata su samu damar yin abin da suke so da bai saba ka’ida ba idan Bola Tinubu ya zama shugaban kasa a Mayu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel