Shugaba Buhari Ya Fadawa Bola Tinubu Alfarmar da Yake Nema a Wajen Gwamnatinsa

Shugaba Buhari Ya Fadawa Bola Tinubu Alfarmar da Yake Nema a Wajen Gwamnatinsa

  • Muhammadu Buhari ya gabatar da jawabi na musamman a wajen taron ranar ma’aikatan Najeriya
  • SGF ya wakilci Shugaban kasa, ya yi kira ga gwamnati mai zuwa ta kula da hakkin ma’aikata
  • Boss Mustapha yana so Asiwaju Bola Tinubu ya kula da dokokin ILO idan ya shiga fadar Aso Rock

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari mai mulkin Najeriya ya ba Asiwaju Bola Tinubu shawarar ya cigaba da mutunta ma’aikatan gwamnatin kasar.

This Day ta ce Mai girma Muhammadu Buhari ya yi wannan kira ne a cikin jawabinsa na murnar zagayowar ranar ma’aikata a ranar 1 ga watan Mayu.

Shugaban kasar mai shirin barin-gado yana so magajinsa ya maida hankali wajen ganin darajar ma’aikata da nufin ganin an kawo cigaba a kasar nan.

Sakataren gwamnatin tarayya, Mista Boss Mustapha ya karanto jawabin a madadin Buhari a jiya.

Kara karanta wannan

Fadar Shugaban Kasa Ta Fitar da Shafuka 90 a Kan Jerin Nasarorin da Buhari Ya Samu

Inda gwamnatin APC ta sa gaba

Shugaban na Najeriya ya ce gwamnatinsa ta yi amanna da cewa kyawun aiki na kwarai shi ne sakayya da albashi mai tsoka da tsare-tsaren morewa aiki.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An ji gwamnati a shirye ta ke wajen rage talauci da samar da hanyar wanzar da adalci, yi da kowa da kawo cigaba mai dorewa da zaman lafiya da tsaro.

Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari Hoto: @BuhariSallauOnline
Asali: Facebook

Muhammadu Buhari ya na so idan wanda za a rantsar ya shiga ofis, ya bi dokokin kwadago watau ILO sau da kafa, hakan zai tabbatar da hakkokin ma’aikata.

A jawabinsa, an rahoto Buhari ya ce yana da kyau gwamnati ta tabbatarwa ma’aikata hakkokinsu, nan da makonni hudu ne zai yi ban-kwana da fadar Aso Villa.

Alkawarin da Bola Tinubu ya dauka

Shi kuma a gefe guda, Bola Tinubu wanda shi ne shugaban Najeriya mai jiran gado ya yi wa ‘yan kwadago alkawarin hada-kai da su, kuma ya taimaka masu.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yari Ya Gana Da Buhari, Ya Ce Arewa Ta Cancanci Shugabancin Majalisar Dattawa

A jawabin da ya gabatar a ranar ma’aikata ta kasa, Tinubu ya yi alkawari gwamnatinsa da za a rantsar a karshen Mayun nan za ta karbo masu hakkokinsu.

NLC: Ayi hattara da IMF

Tribune ta ce kungiyar ‘yan kwadago tayi kira ga gwamnatin tarayya tayi watsi da shawarwarin da IMF ta ke badawa da sunan ceto tattalin arzikin kasa.

Kungiyar ma’aikatan na Najeriya ta ce hukumar bada lamunin na neman kawowa tattalin arzikin Najeriya guba, don haka bai kamata a karbi maganarsu ba.

Masu kudin nahiyar Afrika

A watanni uku aka samu labari babban attajirin nan, Alhaji Abdul Samad Rabiu ya tara abin da ya zarce N270bn, kusan N3bn kenan yake samu a duk rana.

Idan maganar arziki ake yi a Afrika, Aliko Dangote da Johann Rupert ne kadai a gaban Mai kamfanin BUA, Rabiu ya sha gaban Nicky Oppenheimer a yau.

Kara karanta wannan

1 Ga Watan Mayu: Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Litinin a Matsayin Hutu Don Bikin Ranar Ma’aikata

Asali: Legit.ng

Online view pixel