Kotu Ta Umarci DSS Su Fito da Wasu ‘Ya ‘Yan Jam’iyyar PDP 3 da Aka Tsare a Adamawa

Kotu Ta Umarci DSS Su Fito da Wasu ‘Ya ‘Yan Jam’iyyar PDP 3 da Aka Tsare a Adamawa

  • A wata shari’a da aka yi a babbar kotun jihar Adamawa, an umarci DSS ta saki wasu da ta rike
  • Kwanakin baya Jami’an tsaro na fararen kaya suka cafke wasu daga cikin magoya bayan PDP
  • A zaman kotun da aka yi, Christopher Dominic Mapeo ya yi umarni a sake su, kafin a daga kara

Adamawa - Wata babbar kotun jihar Adamawa ta yi zama a game da shari’ar wasu magoya bayan jam’iyyar adawa ta PDP da jami’an tsaro suka cafke.

A rahoton da aka samu daga Daily Trust, an fahimci Mai shari’a Christopher Dominic Mapeo ya yi umarni ga hukumar DSS ta fito da wadannan mutane.

Alkalin da ya saurari karar, Christopher Dominic Mapeo ya umarci DSS masu fararen kaya su saki magoya bayan na jam’iyyar PDP ba tare da wata-wata ba.

Kara karanta wannan

Buhari ya hadu da Gwamnoni a Aso Rock, Ya Nuna Masu Abin da Ya Taimaki Tinubu

A hukuncin da ya zartar a ranar Alhamis, Christopher Mapeo ya ce muddin aka cigaba da garkame wadannan Bayin Allah, hukuma ta sabawa doka.

Za a koma kotu a Mayu

Daily Post ta bayyana cewa Alkalin ya kuma daga shari’ar zuwa 3 ga watan Mayun 2023 lokacin da za a saurari wadanda ake kara domin su kare kan su.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mutumin da ya tsayawa ‘ya ‘yan jam’iyyar ta PDP su uku, Cif L. D. Nzadon ya shigar da kara tun 20 ga watan Afrilu a kotun jihar, yana neman a fito da su.

'Yan DSS
Ana yi wa DSS zanga-zanga Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

L. D. Nzadon ya shigar da mabanbatan bukatu a kan kowane daga cikin wadanda aka daure.

Lauya ya san halin DSS

Da yake magana bayan an dawo zaman kotu a jiya, Lauyan ‘yan siyasar, Abayomi Akamode ya shaida cewa DSS ta aika masu sako su zo su karbi beli.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya Ta Kashe Naira Miliyan 560 Wajen Ceto ‘Yan Najeriya a Kasar Sudan

Abayomi Akamode yake cewa ba su so jami’an tsaron masu fararen kaya su yaudare su, saboda haka su ka nemi Alkali ya yi amfani da karfinsa, ya sake su.

Shi kuwa U. F. Ahmed a matsayinsa na Lauyan wanda ake tuhuma bai ja da hukuncin kotu ba. Sahara Reporters ta fitar da labarin nan a daren yau.

Iyakar ta Ahmed ya bukaci a daga shari’ar zuwa wani lokaci nan gaba domin samun damar da za su gabatar da hujjojinsu gaban Alkalin kotun da yake Yola.

Mata a siyasar Najeriya

Ana da labari cewa mutum 15000 suka samu tikiti, suka fito takara a 2023, a cikinsu mata 72 suka ci zabe, hakan ya nuna 96% na mata ba su kai labari ba.

Ko da Ireti Kingibe za ta zama Sanata, irinsu Natasha Akpoti da suka yi takara ba su kai labari ba, haka abin yake ga Khadijah Abdullahi Iya a zaben bana.

Kara karanta wannan

Peter Obi Ya Ankarar da Kotu a Kan Babbar ‘Hujjar’ da ke Nuna Magudin Bola Tinubu

Asali: Legit.ng

Online view pixel