Yadda Mafi Yawan Matan da Suka Shiga Takara a Zaben 2023 Suka Kifo Ta Kai

Yadda Mafi Yawan Matan da Suka Shiga Takara a Zaben 2023 Suka Kifo Ta Kai

  • Akasarin matan da aka tsaida takara a zaben tsaida gwani, ba su samu nasara a zaben da ya gabata ba
  • Matan da aka doke sun ce siyasar daba da amfani da kudi wajen sayen kujerar siyasa shi ne matsalar
  • Mafi yawan wadanda ake shirin rantsarwa a Majalisa da Gwamnoni maza ne, adadinsu ya kai 96%

Abuja - Bincike ya nuna 96% na matan da suka shiga takara domin samun mukaman siyasa a zaben da ya gabata a kasar nan, ba su iya kai labari ba.

Daily Trust da ta gudanar da wannan bincike ta ce akwai mata fiye da 1, 500 da suka fita takara a zaben shugaban kasa, gwamnoni da kuma na majalisa.

A cikin mutane 15,307 da suka tsaya takara a zaben 2023, 89.8% dinsu maza ne, mata 10.1% ne kawai, sannan daga cikin matan, 72 rak suka lashe zabe.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Bayan Shekaru 8 Da Aure Tare Da Yara 2, Ma’aurata Sun Gano Su Din Yan’uwa Ne, Bidiyon Ya Yadu

A sanarwar da hukumar zabe ta kasa watau INEC ta bada, mata 1,487 da suka yi takara, ba su yi nasara ba, mafi shahara ita ce Aisha Dahiru Binani.

Matan da suka yi nasara

Matan da za a rantsar a ranar 29 ga watan Mayu sun hada da bakwai da za su zama mataimakan Gwamnoni, 14 a majalisar wakilai da kuma Sanatoci uku.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A majalisar dokokin jiha, za a rantsar da mata 48 a cikin mutane fiye da 900 da suka yi takara.

Binani
Aisha Dahiru Binani Hoto: newswirengr.com
Asali: UGC

Kusan haka abin yake ko a zaben 2019, rahoton ya ce mata 2, 970 aka tsaida a matsayin ‘yan takara a jam’iyyun siyasa, amma 62 kadai suka yi galaba

98% na matan da aka gwabza da su a zaben 2019 sun kunyata, amma a wannan karo an fi samun adadin matan da za su zama mataimakan Gwamnoni a jihohi.

Kara karanta wannan

Babu Murdiya, Babu Magudi – Minista Ya Ambaci Silar Nasar Tinubu a Zaben 2023

Ya aka yi haka?

‘Yar takarar Gwamnar jihar Jigawa a jam’iyyar AA, Binta Umar ta shaidawa jaridar cewa ta zargi mata da hadin-kai, ta ce adadinsu ya kai su iya lashe zabe.

Binta ta koka a kan yadda ake amfani da kudi wajen sayen kujerar siyasa, sannan ta ce al’ada da addini su na cikin abubuwan da su ke hana mata karbuwa.

‘Yar takarar Gwamnar Neja a APGA a zaben bana, Khadijah Iya Abdullahi ta ce saba doka da INEC ta yi da kuma magudin zabe suka jawo ta gagara cin zabe.

Matan da suka nemi takara sun nuna takaicinsu a kan siyasar kudi da daba da ake yi a Najeriya, suka ce a dalilin haka ne takwarorinsu ba su samun mulki.

Mata da suka shahara a siyasa

A kusan ko ina, ana kukan maza sun karbe fagen siyasa, ba a barin mata su na samun mukami, rahotonmu ya nuna akwai wadanda suka fita zakkah.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Wani gini ya ruguje a barikin 'yan sanda, ya kashe, ya danne mutane da yawa

Daga cikin wadannan mata akwai Aisha Dahiru Binani wanda ta nemi takarar Gwamna a Adamawa da Marigayiya Sanata Aisha Jummai Alhassan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel