Gwamnan Gombe Ya Rushe Majalisar Zartaswa, Ya Ba Su Wa'adin Barin Ofis
- Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya sallami dukkan mambobin majalisar zartaswan gwamnatinsa
- A wata sanarwa daga Ofishin sakataren gwamnatin, Yahaya ya ɗauki wannan matakin ne saboda karewar wa'adin zangon farko
- Ya umarci duk wanda matakin ya shafa ya miƙa ragamar ma'aikata, ɓangare ko hukumar da yake jagoranta ga Sakatarensa
Gombe - Gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya rushe majalisar kwamishinoni da hadimansa, kuma ya roki dukkan waɗanda abun ya shafa su shirya barin Ofis.
Punch ta tattaro cewa gwamna Yahaya ya umarci dukkan naɗe-naɗen mambobin majalisar su rubuta takardar miƙa ragamar ma'aikatar da suke jagoranta gabanin ranar Laraba 19 ga watan Afrilu, 2023.

Source: UGC
Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa mai ɗauke da kwanan watan 11 ga watan Afrilu, 2023, kuma an mata take da, "Miƙa ragamar ma'aikatu, sashi-sashi da hukumomi."

Kara karanta wannan
Shin An Biya Kuɗin Fansa? Ɗalibai Mata Na Jami'ar Tarayya Gusau Sun Kubuta Daga Hannun Yan Bindiga
Sanarwan na ɗauke da sa hannun Rabiu Abubakar, a madadin ofishin Sakataren gwamnatin jihar Gombe.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Abubakar ya bukaci dukkan mambobin majalisar zartaswa da wannan mataki ya shafa su miƙa ragamar wurin da suke shugabanta hannun babban sakataren da ya dace da ma'aikatunsu.
Meyasa gwamna ya ɗauki wannan matakin?
Ya bayyana cewa gwamna Yahaya ya ɗauki wannan mataki ne sakamakon nasarar da ya samu a a zaben gwamnan da aka kammala, wanda ya kawo karshen zangon mulkinsa na farko.
Sanarwan ta ce:
"Biyo bayan kammala zaɓen gwamnan 2023 wanda ya kawo karshen zangon farko na mulkin gwamna Muhammad Inuwa Yahaya (Ɗan Majen Gombe). An umarci na bukaci ku shirya bayanan miƙa ma'aikata, ɓangare da hukumomi."
"Bayanan da zaku rubuta ya ƙunshi duk wasu ayyuka da tsare-tsaren gwamnati da ba'a kammala ba. Muna bukatar ku miƙa bayanan Ofishin Sakataren gwamnati kafin ko ranar Laraba 19 ga watan Afrilu, 2023."
A wani labarin kuma Wani Gwamna Ya Dira Yola, Ya Yi Kus-Kus da Fintiri Kan Ayyana Binani a Matsayin Gwamnan Adamawa
Gwamnan jihar Oyo ya ziyarci takwaransa na jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri a gidan gwamnatinsa da ke Yola, babban birnin jihar.
Bayan ganawar gwamnonin 2, Seyi Makinde, ya yaba da namijin kokarin INEC a jihar Oyo, amma ya bukaci ta gaggauta gyara kuskurenta a jihar Adamawa.
Asali: Legit.ng
