Jam'iyyar APC Ta Dakatar da Ɗan Majalisar Wakilan Tarayya a Jihar Kebbi

Jam'iyyar APC Ta Dakatar da Ɗan Majalisar Wakilan Tarayya a Jihar Kebbi

  • Kwana ɗaya gabanin zaɓen ciko, jam'iyyar APC a jihar Kebbi ta dakatar da ɗan majalisar wakilan tarayya kan zargin cin amana
  • Shugaban jam'iyya ya ce sun karɓi korafe-korafe daban-daban daga mambobin mazaɓarsa kan ayyukan da yake aikatawa
  • A gobe Asabar 15 ga watan Afrilu, 2023, INEC zata gudanar da karishen zaɓen gwamna a jihar Kebbi da wasu sassan kasar nan

Kebbi - Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a jihar Kebbi ta dakatar da ɗan majalisar wakilan tarayya, Honorabul Shehu Muhammed Koko.

A bayanan da jaridar The Nation ta tattaro, jam'iyyar APC ta ɗauki wannan matakin ne kan zarginsa da yi mata zagon ƙasa a zaɓe.

Jam'iyyar APC.
Jam'iyyar APC Ta Dakatar da Ɗan Majalisar Wakilan Tarayya a Jihar Kebbi Hoto: thenation
Asali: UGC

Shugaban APC reshen jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya, Alhaji Abubakar Muhammad Kana, shi ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya rattaɓa wa hannu da kansa.

Kara karanta wannan

Ana Gobe Zabe, Jam'iyyar PDP Ta Dakatar Da Shugabanta Da Mataimakinsa a Wata Babbar Jiha

Ya ce sun samu korafe-korafe daga mambobin jam'iyya daga yankin ƙaramar hukumar Koko-Basse kan zargin da ake wa ɗan majalisar na cin amana da zagon ƙasa, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa, korafin da suka karɓa ya nuna ayyukan Honorabul Bako ka iya haddasa ta da yamutsi da kuma durƙusad da jam'iyya, da kuma rashin bin umarnin na gaba.

Shugaban jam'iyyar ya ƙara da cewa ayyukan ɗan siyasan sun zama barazana ga zaman lafiya, haɗin kai da dunƙulewar jam'iyyar APC a jihar Kebbi.

"Hakan ya yi hannun riga da manufa da kudirin jam'iyyar APC kuma ya saɓa wa tanadin sashi na 21 (2) (I) (Ii) (vi) (vii) da ke ƙunshe a kundin dokokin jam'iyya."
"Muna sanarwa ɗaukacin al'umma cewa kwamitin gudanarwa na jiha ya amince da matakin dakatar da Honorabul Shehu Muhammed Koko, daga harkokin APC har zuwa lokacin da za'a kammala bincike."

Kara karanta wannan

Ana Saura Awanni 24: Atiku Ya Yi Magana Mai Jan Hankali Game da Cikon Zaɓen Gwamna a Adamawa da Kebbi

- inji shugaban APC na Kebbi, Alhaji Abubakar Muhammad Kana.

Gwamna Tambuwal Ya Nada Sabbin Ciyamomi

A wani labarin kuma Bayan Ya Sha Kaye Hannun APC, Gwamna Tambuwal Na PDP Ya Naɗa Sabbin Ciyamomi 23

Gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ya naɗa sabbin shugabanni a kananan hukumomi 23 watau Kantomomi.

Sakataren gwamnatin jihar ya ce naɗin ya fara aiki tun ranar 11 ga watan Afrilu, 2023 kuma ya bayyana sunayen sabbin kantomomin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel