Magana Ta Koma Kotu, Binani Ta Nemi a Tsaida Tattara Sakamakon Zaben Adamawa

Magana Ta Koma Kotu, Binani Ta Nemi a Tsaida Tattara Sakamakon Zaben Adamawa

  • Aisha Dahiru Binani ta kai kara domin Kotu tayi umarnin dakatar da aikin zaben Jihar Adamawa
  • ‘Yar takarar APC ta ce a fasa tattara sakamakon zabe, Kotun tarayya ta raba mata gardama da INEC
  • Lauyoyin Binani sun zargi Gwamna Ahmadu Fintiri da kawo hayanyi da jin zarafin jami’in INEC

Abuja - Aisha Dahiru Ahmed Binani, ta dumfari babban kotun tarayya mai zama a garin Abuja domin tsaida tattara zaben gwamnan jihar Adamawa.

Vanguard ta ce Aisha Dahiru Ahmed ‘Binani’ ta shigar da kara mai lamba FHC/ABJ/CS/510/2023, ta na so kotu ta raba gardamar rudanin aka burma.

Sanata Aisha Dahiru Ahmed Binani ta na so a haramtawa Hukumar INEC da jami’anta daukar wani matakin a kan zaben Gwamnan Adamawa.

‘Yar takarar Gwamnan ta bukaci kotun da ke zama a birnin tarayya ta soke matsayar da INEC ta dauka bayan wani Kwamishina ya ayyana nasararta.

Kara karanta wannan

Majalisar dattawa: APC ta lashe kujeru 59, an fadi yawan na PDP, NNPP, LP da SDP

An yi karar Gwamna da PDP

The Cable ta ce Binani wanda ta ke takara a karkashin jam’iyyar APC ta na so kotu ta duba lamarin, a cewarta kotu kadai za ta iya soke zaben da aka lashe.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yayin da jam’iyyar APC ta ke cikin masu suka shigar da kara, Hussain Zakariyau, SAN ya hada INEC, PDP da Ahmadu Fintiri cikin masu kare kan su.

Zaben Adamawa
Sanata Aisha Binani wajen kamfe Horo: @MBuhari
Asali: Twitter

Zargin da ke wuyan Gwamna da jam’iyyarsa shi ne jawo hargitsi da jin zarafin ma’aikacin INEC. Bangaororin za su dauki lauyoyi domin kare kansu.

Legit.ng Hausa ta fahimci karar ta je gaban kotun a ranar Litinin, 17 ga watan Afrilu, amma ba mu da masaniyar ko an tsaida lokacin fara sauraron shari’a.

Ikirarin da Lauyan APC yake yi

Lauyan da ya shigar da kara a matsayin ‘yar takarar APC da jam’iyya mai-ci, Hussain Zakariyau, ya kafa hujja da sashe na 251 (1)q & r na tsarin mulkin 1999.

Kara karanta wannan

Labari Mai Zafi: Dino Melaye Ya Samu Takarar Gwamnan Jihar Kogi a Jam’iyyar PDP

Tashar Channels ta ce babban lauyan ya yi hujja da sassa na 149 & 152 na dokar zabe wajen shigar da karar, yana rokon a fasa ayyana wanda ya lashe zaben.

Abin da lauyan yake cewa shi ne INEC ta shiga lamarin da ya fi karfinta da ta soke sanarwar da aka yi, ya ce wannan aikin kotun sauraron karar zabe ne.

Kwamacala a Adamawa

A yayin da ake karasa zaben Adamawa, an ji babban Kwamishinan INEC ya sanar da ‘yar takarar APC a matsayin wanda tayi nasara, kafin a tsaida zaben.

Asali: Legit.ng

Online view pixel