Zaben Adamawa da Kebbi: Atiku Ya Ja Hankalin Mutane Su Zabi PDP

Zaben Adamawa da Kebbi: Atiku Ya Ja Hankalin Mutane Su Zabi PDP

  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi magana kan cikon zaben da za'a gudanar a Adamawa da Kebbi
  • Alhaji Atiku ya yi kira ga masu kaɗa kuri'a a jihohin biyu su fito kwansu da kwarkwata su dangwala wa PDP
  • A gobe Asabar 15 ga watan Afrilu, 2023, INEC zata gudanar da cikon zaɓen gwamna a jihohin 2

Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar PDP a zaben 25 ga watan Fabrairu, 2023, Alhaji Atiku Abubakar, ya roki masu kaɗa kuri'a a jihohin Adamawa da Kebbi.

Premium Times ta rahoto cewa ranar Alhamis, Atiku ya roki masu katin zaɓe su zaɓi PDP a ƙarishen zaɓen gwamnan da za'a gudanar ranar 15 ga watan Afrilu, 2023 a Adamawa da Kebbi.

Alhaji Atiku Abubakar.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar Hoto: Atiku Abubakar
Asali: UGC

Hukumar zaɓe INEC ta sanya ranar Asabar 15 ga watan Afrilu domin ƙarisa zaben gwamna a jihohin 2, kuma a mazaɓun Sanatoci 5, mambobin majalisar wakilai 31, yan majalisar jiha 58.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Ya Ayyana Kudirin Neman Tazarce a Zaben Jiharsa Da Ke Tafe 2023

Wannan kiran da Atiku ya yi na a dangwala wa jam'iyyar PDP na ƙunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Mista Paul Ibe, ya fitar a birnin tarayya Abuja.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tsohon mataimakin shugaban kasan ya kuma roki masu kaɗa kuri'a da su tabbatar da zaman lafiya a tsakaninsu lokacin da kuma bayan wannan zaɓe da za'a yi.

A rahoton Vanguard, Atiku ya ce:

"A jihohin Adamawa da kuma Kebbi, inda za'a gudanar da cikon zaɓe, ina kira ga masu kaɗa kuri'a su tabbata jam'iyyar PDP ta samu dukkan goyon bayan da take buƙata."

A jihar Adamawa inda Atiku ya fito, fafatawa ta yi zafi tsakanin gwamna mai ci na jam'iyyar PDP, Ahmadu Fintiri, da kuma yar takarar gwamna a inuwar APC, Sanata Aishatu Binani.

Bayan kammala tattara sakamako daga kananan hukumomi 21, baturen zaɓen INEC ya ce zaben bai kammalu ba saboda tazarar dake tsakanin yan takara 2 ba ta kai yawan kuri'un da aka soke ba.

Kara karanta wannan

Zargin Ta'addanci: Shugaban Masu Rinjaye Na Majalisar Dokoki a Arewa Ya Yi Murabus, An Naɗa Sabo

A wani labarin kuma mun tattara muku Jerin Sanatocin Arewa Da Ke Neman Kujerar Shugaban Majalisar Dattawa

Nan da wata ɗaya da 'yan kwanaki, shugaban kasa Muhammadu Buhari, zai sauka daga mulki bayan karewar wa'adinsa, Tinubu zai karba.

Sai dai tun yanzun Yan majalisu sun fara kokarin neman shugabanci a majalisa ta 10 da za'a rantsar karkashin mulkin Tinubu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel