Bikin Rantsarwa: Kotu Ta Ki Ba Da Belin Mai Zanga-Zangar Adawa Da Tinubu a Jirgin Sama

Bikin Rantsarwa: Kotu Ta Ki Ba Da Belin Mai Zanga-Zangar Adawa Da Tinubu a Jirgin Sama

  • Kotu ta hana mutumin da ya yi zanga-zangar adawa da bikin rantsar da Bola Tinubu a matsayin shugaban kasa beli
  • Obiajuli Uja wanda ya kasance fasinja a wani jirgin sama ya kekyashe kasa ya ce sam ba za a rantsar da Tiunubu ba a ranar 29 ga watan Mayu
  • Mai shari'a Mohammed Abdulazeez Ismail ya nemi a garkame shi a gidan gyara hali na Kuje

Abuja - Wata kotun majistare da ke zama a yankin Zuba ta birnin tarayya, Abuja, ta ki bayar da belin fasinjan jirgin sama da ya yi zanga-zangar cewa ba za a rantsar da Tinubu ba a yan makonni da suka gabata.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa kotun ta mika Obiajuli Uja, wanda ya yi furucin mai matukar jan hankali game da Bola Tinubu, zababben shugaban kasa, a cikin jirgin sama da zai tashi daga Abuja zuwa Lagas ga yan sanda.

Kara karanta wannan

Bikin Easter Na 2023: Bishop Kuka Ya Aike Da Kakkausan Sako Ga Buhari, Tinubu Da Kotun Koli

Mai adawa da bikin rantsar da Tinubu da zababben shugaban kasa
Bikin Rantsarwa: Kotu Ta Ki Ba Da Belin Mai Zanga-Zangar Adawa Da Tinubu a Jirgin Sama Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Alkali Mohammed Abdulazeez Ismail ya zartar da hukunci

Da yake zartar da hukunci a kan bukatar neman belin da lauyan Uja ya gabatar, alkalin kotun, Mohammed Abdulazeez Ismail, ya bayyana cewa bukatar ya yi wuri da yawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar alkalin, abubuwan da aka gabatar tare da bukatar Uja bai nuna cewa wanda ake karar bai da lafiyar da zai iya fuskantar shari'a ba illa ya nuna cewa zuciyarsa bata da nutsuwa sosai.

Ismail ya bayyana cewa koda dai kundin tsarin mulki ya bai wa kowani dan Najeriya yanci, kotu na da ikon hana mutum yancinsa bisa dalilai na lafiya, rahoton The Sun.

Da yake nuni ga tanadin sashi 35(1)(e) na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 (kamar yadda aka gyara ta) da sashi 278 na dokar laifi (ACJA), 2015, alkalin kotun ya ce ba za a iya ba Uja beli ba.

Kara karanta wannan

Biyu Babu: Wani Ya Damfari Yar Gidan Magajiya A Abuja, Bai Biya Ta Kudin Aiki Ba Kuma Ya Sace Wayarta

Ya riki cewa a inda lafiyar kwakwalwar wanda ake kara ya zama matsala, kotun ke da alhakin tabbatar da yanayin lafiyar wanda ake karar.

Don haka ya ki bayar da belin mutumin sannan ya umurci a garkame Uja a gidan gyara halin Kuje.

Ya kuma yi umurnin cewa shugaban cibiyar ya dauki wanda ake karar zuwa wani asibitin gwamnati don tabbatar da lafiyar kwakwalwarsa.

Daga nan sai ya dage shari'ar har zuwa 20 ga watan Afrilu don ci gaba da sauraronsa.

Ba za a rantsar da Tinubu ba, magoyin bayan Peter Obi ya yi zanga-zanga

A baya mun kawo cewa wani mutum ya kawo tsaiko yayin da wani jirgin sama ke gab da tashi daga Abuja zuwa Lagas inda ya ce sam ba za a rantsar da Bola Tinubu ba a matsayin shugaban kasa a ranar 29 ga watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel