Bikin Easter Na 2023: Bishop Kuka Ya Aike Da Kakkausan Sako Ga Buhari, Tinubu Da Kotun Koli

Bikin Easter Na 2023: Bishop Kuka Ya Aike Da Kakkausan Sako Ga Buhari, Tinubu Da Kotun Koli

  • A sakonsa na bikin ranar Easter, Bishop Kuka ya yi addu'a ga Shugaba Buhari yayin da ya ke dab da kammala wa'adin sa, yana ba shi shawara ya cika aikinsa
  • Malamin ya bayyana damuwa game da amfani da karfin shari'a da wasu yan siyasa ke yi yana rokon alkalan kotun koli da su kare kima da martabarsu
  • Kukah ya kuma bukaci zababben shugaban kasa Tinubu, ya na shawartarsa da ya mayar da hankali kan walwalar yan Najeriya, yaki da rashawa da nuna wariya

Sokoto - Bishop din Katolika na Sokoto, Matthew Hassan Kukah, ya roki Allah, ya bada kariyarsa ga Shugaba Muhammadu Buhari yayin da ya ke dab da kammala wa'adin mulkinsa ranar 29 ga watan Mayu, 2023.

A sakonsa na bikin Easter 2023, ya bukaci zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, cewa ba gine gine ba ne ko batun raba mukamai ne a gaban Najeriya ba, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

“Kasuwa Bata Yi Mun Dadi Ba”: Gwamnan Arewa Ya Magantu Kan Faduwa Da Ya Yi a Zaben Sanata

Kukah, Buhari, Tinubu da CJN
Bikin Easter 2023: Bishop Kuka Ya Aike Da Kakkausan Sako Ga Buhari, Tinubu Da Kotun Koli. Hoto: Bishop Kukah, Femi Adesina, Bola Tinubu
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Malamin mara tsoro ya kuma aike da sako ga alkalan kotun kolin Najeriya, wanda ke kula da shari'ar zabukan da aka gudanar a zaben 2023 cewa yan Najeriya sun zuba mu su ido.

Kotun koli: Yan siyasa na kokarin amfani da karfin shari'a - Kukah

Bishop Kukah ya bayyana damuwarsa game da yadda yan siyasa su ke amfani da karfin shari'a, wanda ke janyo rashin tabbas ga kasa game da kotunan.

Ya roki alkalai da su kare mutunci da kimarsu ta hanyar yanke hukuncin adalci bisa abin da doka ta tanada.

"Muna rokon Allah ya ba ku hikima ku ga meye daidai da karfin ikon gudanar da hukuncin gaskiya" in ji Kukah.

Sakon Kukah ga zababben shugaban kasa Tinubu

A daya bangaren, Bishop Kukah ya ce yana fatan Tinubu zai fahimci bukatar yan Najeriya na samar da walwala ga yan kasa.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Buhari Ya Bayyana Abun da Ya Kamata Atiku, Peter Obi da Sauransu Su Yi

Yayi kira a hada kai, a tafi tare, da yancin barin kowa ya gudanar da addini, ya na rokon kasar ta farfado daga kuncin rashawa.

Ya kuma bayyana bukatar a kawar da wariya da bambancin addinai don samun makoma mai kyau.

"Ina fatan kai (zababben shugaban kasa) zaka fifita babban aikin da ke gabanka ba na rabon mukamai ba. Akwai mafi mahimmanci, ka bar mu a raye saboda iya masu raine za su more ayyuka," in ji shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel