Dan Majalisar NNPP Ya Fayyace Gaskiya Kan Wanda Yakamata Ya Zama Shugaban Majalisa Ta 10

Dan Majalisar NNPP Ya Fayyace Gaskiya Kan Wanda Yakamata Ya Zama Shugaban Majalisa Ta 10

  • Abdulmumin Jibrin yayi tsokaci kan wanda yakamta ya zama shugaban majalisar dattawa ta 10
  • Zaɓaɓɓen ɗan majalisar yace wannan muƙamin bai kamata ya koma hannun musulmi ɗan Arewa ba
  • Abdulmumin yace shugabancin majalisar kamata yayi ya koma hannun kirista daga Kudancin Najeriya

Jihar Kano- Zaɓaɓɓen ɗan majalisar wakilai ta tarayya, Abdulmumin Jibrin, yace musulmi ɗan Arewacin Najeriya bai kamata ya zama shugaban majalisar dattawa ba.

Da yake magana a ranar Laraba a wata tattaunawa da gidan Talbijin na Channels Tv, Jibrin ya bayyana cewa jam'iyyar NNPP a Kano ta koyawa gwamna Ganduje darasin siyasa wanda ba zai taɓa mantawa da shi ba a rayuwar sa.

Jibrin
Dan Majalisar NNPP Ya Fayyace Gaskiya Kan Wanda Yakamata Ya Zama Shugaban Majalisa Ta 10 Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Jibrin yace idan aka yi duba da abinda ya faru a 1999, shugaban majalisar dattawa na gaba kamata yayi ya fito daga yankin Kudu maso Gabas. Rahoton The Cable

Kara karanta wannan

Watanni 2 Gabanin Ya Sauka Daga Mulki, Gwamnan PDP Ya Ƙara Jika Wa Zababɓen Gwamna Aiki

Abdulmumin Jibrin zai wakilci mazaɓar Kiru/Bebeji daga jihar Kano a majalisar wakilai ta 10.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kafin rantsar da majalisa ta 10 a watan Yuni, zaɓaɓɓun ƴan majalisa sun fara zawarcin neman kujerun shugabancin majalisar wakilai da ta dattawa.

Tun da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Tinubu da mataimakin sa Kashim Shettima, musulmai ne, ana ta bayar da shawarwarin ganin an samar da daidaito a shugabancin majalisun tarayya.

Da yake magana aka lamarin, Jibrin ya bayyana cewa muƙamin mataimakin majalisar dattawa da na kakakin majalisar wakilai, kamata yayi a ba yankin Arewa ta tsakiya da yankin Arewa ta Yamma.

"Ra'ayin ƙashin kai na shine idan ka dubi gabaɗaya rigimar dake tattare da tikitin Muslim-Muslim, duk wanda yake son ƙasar nan bai kamata ya riƙa tunanin cewa musulmi ɗan Arewa ya zama shugaban majalisar dattawa ba." Inji shi

Kara karanta wannan

Sirri Ya Fasu: An Gano Sunan Gwamnan Arewa da Wasu Mutum 2 da Tinubu Zai Ba Manyan Muƙamai Na Farko

"Abinda yafi dacewa shine muƙamin yaje hannun kirista ɗan yankin Kudancin Najeriya. Nayi amanna cewa duk wanda baya son hakan yafi son kansa fiye da ƙasar nan."

Fafutukar Neman Shugabancin Majalisa: Manyan Yan Majalisar Wakilai 3 Suna Goyon Bayan Wase

A wani labarin na daban kuma, wasu manyan ƴan majalisar wakilai 3 sun bayyana wanda suke goyon bayan ya zama shugaban majalisar wakilai ta 10.

Ƴan majalisar sun nuna goyon bayan su ga Ahmed Idrsi Wase ya zama shugaban majalisar na gaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel