Fafutukar Neman Shugabancin Majalisa: Manyan Yan Majalisar Wakilai 3 Suna Goyon Bayan Wase

Fafutukar Neman Shugabancin Majalisa: Manyan Yan Majalisar Wakilai 3 Suna Goyon Bayan Wase

Kulla-Kullan da jam'iyyar PDP ke yi na hada kan mambobinta da sauran marasa rinjaye a majalisa don samun karfi gabannin rantsar da majalisa ta 10 ya hadu da babban cikas.

Manyan jiga-jigan PDP biyu, Gwamna Nyesom Wike da tsohon gwamnan jihar Delta, James Ibori sun ayyana goyon bayansu ga mataimakin kakakin majalisar wakilai, Ahmed Idris Wase.

Baya ga su, tsohon gwamnan jihar Osun, Olusegun Osoba ma ya bayyana Wase a matsayin dansa abun soyuwa a gare shi wanda yankinsa, arewa ta tsakiya ya cancanci mukamin kakakin majalisa.

Manyan yan siyasan uku sun bayar da goyon bayansu ga Wase yayin da ya yi zarya daga Abuja zuwa Lagas-Port Harcourt-Abuja a ranar Litinin, jaridar The Nation ta rahoto.

Ahmed Wase tare da Nyesom Wike
Fafutukar Neman Shugabancin Majalisa: Manyan Yan Majalisar Wakilai 3 Suna Goyon Bayan Wase Hoto: The Dream Daily
Asali: UGC

Wannan ci gaban na zuwa ne yayin da ake tsaka da tattaunawa don yin hadaka tsakanin yan majalisar wakilai na PDP da wani dan takarar kujerar kakakin majalisar a bangare daya, da kuma PDP da sauran jam'iyyu marasa rinjaye a daya bangaren.

Kara karanta wannan

'Jam'iyyar APC da Mambobin Majalisa Sun Nuna Wanda Suke So Ya Zama Kakakin Majalisar Wakilai'

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake tunanin cewa jam'iyyarsa ta APC na iya mika mukamin a wajen yankinsa, an tattaro cewa dan majalisa daga arewa maso gabas ya shiga tattaunawa da yan PDP domin su mara masa baya gabannin takarar.

Sai dai kuma, abun da bai sani ba shine manyan jiga-jigan PDP musamman mambobin majalisar masu dawowa, suna shirin dunkulewa da sauran jam'iyyu wajen shan gaban APC a takarar.

Adadin jam'iyyun adawa ya fi na APC mai mambobi 162. PDP na da kujeru 102, LP na da kujeru 34, NNPP na da kujeru 18, APGA na da kujeru hudu yayin da SDP da ADC ke da kujeru biyu kowannensu.

Dangane da sakamakon zaben cike gurbi na ranar 15 ga watan Afrilu a fadin wasu jijojin, jam'iyyun adawa na da jimilar kujeru 163. Za a yi zaben cike gurbi a mazabu 33 a fadin kasar.

Kara karanta wannan

Rikici Ya Dawo Ɗanye, APC Ta Dakatar da Shugaban Jam'iyya Da Wani Babban Jigo

Martanin Ibori kan takarar Wase

Yayin da yake tarban mataimakin kakin majalisar wakilan, Ibori ya ce ya yanke shawarar umurtan magoya bayansa wadanda suke mambobin majalisa da su marawa Wase baya sannan su zabe shi.

Ibori ya ce:

"Ina tare da kai; na yi bincikena a kanka kuma na gamsu ka shirya ma aikin kuma na yi farin ciki da zuwanka nan ko da dai na aika maka sako ta mambobin majalisarmu cewa su je da kai. Ina maka fatan alkhairi.
"Kada ka yi kasa a gwiwa wajen zuwa gareni a duk lokacin da kake bukatar wani abu da zai karfafa wannan aiki. Zan ci maka albasa a wajen dukkan abokaina. Da dama suna jira don yin abun da ya dace don sa sauranm kasashen Afrika da duniya yin kishi da Najeriya. Ci gaba da gashi, kana kan hanya."

Martanin Osoba game da takarar Wase

A nashi bangaren Osoba wanda ya ce arewa ta tsakiya ta cancanci mukamin ya bayyana Wase a matsayin dansa abun sonsa.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Gwamna Wike Bai Hakura Ba, Ya Kara Dauko Hanyar Ruguza Jam'iyyar PDP

Ya ce:

"Nan gidanka ne; kana da gogewa kuma kai dana ne mafi soyuwa a gareni. Arewa ta tsakiya na da matukar muhimmanci a nasarar zaben APC. Arewa ta tsakiya ta cancanci zama kakakin majalisar wakilai. Ya zama dole mu ba da tikwici ga masu kokari.
"Don haka, a kan arewa ta tsakiya, wannan ya kamata a yi; ina mai baka tabbaci. Za a tura yankin arewa ta tsakiya kuma daga nan ne za mu shiga mataki na gaba. Wase, kai dana ne abun sona, na kara maimaitawa."

Wike ya jaddada goyon bayansa ga Wase

Yayin da yake yi wa Wase maraba da zuwa gidan gwamnati a Port Harcourt, Wike ya jaddada hukuncinsa na hada kai da gwamnatin da ke sama, rahoton The Cable.

"Babu mai bi na bashin hakuri, na sha fadi cewa zan marawa jam'iyyarka baya a matsakin kasa. Kai mutum ne mai gogewa, mutanenmu za su mara maka baya, za ka daidaita majalisar kuma muna bukatarka. Za mu baka goyon bayan da ya dace da kuma tabbatar da nasararka; ka yarda da mu."

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Gwamnoni 36 Za Su Gana Da EFCC, CBN Don Yanke Shawara Kan Kudin Tsaro

Kiristan kudu ne ya kamata ya zama shugaban majalisar dattawa

A wani labarin kuma, mun ji cewa wani dan majalisa ya tofa albarkacin bakinsa game da wanda ya kamata ya zama shugaban majalisar dattawa, inda ya ce kiristan kudu ne ya cancanci hawa wannan kujera.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng