Gwamnan Abiya Ya Nada Shugaban Ma'aikatan Fadar Gwamnatinsa

Gwamnan Abiya Ya Nada Shugaban Ma'aikatan Fadar Gwamnatinsa

  • Gwamna Okezie Ikoeazu na jihar Abiya ya naɗa sabon shugaban ma'aikatan fadar gwamnatinsa, ya ce naɗin zai fara nan take
  • Wannan na zuwa ne kusan mako ɗaya da gwamnan ya kori hadimansa daga bakin aiki gabanin zuwan ranar miƙa mulki
  • A ranar 29 ga watan Mayu, 2023 za'a rantsar da zababbun yan takarar da suka ci zaɓe a babban zaben 2023 da aka kammala

Abia - Gwamnan jihar Abiya da ke kudu maso gabashin Najeriya, Okezie Ikpeazu ya naɗa Chukwuemeka Enwereji a matsayin sabon shugaban ma'aikatan gidan gwamnati.

Channels tv ta rahoto cewa wannan naɗin na kunshe ne a wata sanarwa da Sakataren watsa labaran gwamna, Onyebuchi Ememanka, ya fitar ranar Laraba.

Gwamna Ikpeazu.
Gwamnan Abiya Ya Ɓada Shugaban Ma'aikatan Fadar Gwamnatinsa Hoto: channelstv
Asali: UGC

A cewar sanarwan, Enwereji, na da shaidar kammala karatun digirin farko a fannin sanin doka "Lawa" a jami'ar jihar Abiya. Ya yi digiri na biyu a Law a jami'ar Legas.

Kara karanta wannan

Jerin Sunayen Gwamnonin da Suka Fara Takun Saƙa da Waɗanda Zasu Gaje Su Tun Kafin Miƙa Mulki

Haka nan kuma ya yi makarantar horar da Lauyoyi kuma an rantsar da shi a matsayin cikakken lauya masanin doka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

"Masani kan harkokin shige da ficen kuɗi, Mista Enwereji ya rike kujerar Sakatare daga bisani Janar Manajan a kamfanin Travelex, sai kuma bangaren hada-hadar kuɗi."
"A sabon muƙamin da aka naɗa shi, Mista Enwereji, zai yi ƙoƙarin tara duk wasu bayanan harkokin da aka gudana a Ofishin gwamna da tabbatar da gwamnatinsa ta miƙa mulki lafiya."

Mai magana da yawun mai girma gwamnan ya ce naɗa sabon shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin Abiya zai fara aiki nan take, kamar yadda Daily Post ta rahoto.

Gwamna ya kori baku ɗaya hadimansa

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa a ranar Alhamis ɗin da ta gabata, Gwamna Ikpeazu, ya amince da korar baki ɗaya naɗe-naɗen siyasar da ya yi nan take.

Kara karanta wannan

Rikici Ya Dawo Ɗanye, APC Ta Dakatar da Shugaban Jam'iyya Da Wani Babban Jigo

Daga cikin waɗanda matakin ya shafa sun haɗa da masu taimakawa na nusamnan, manyan mataimaka na musamman, mashawarta na musamman da sauransu.

A wani labarin kuma Jam'iyyar APC da Mambobin Majalisa Sun Nuna Wanda Suke So Ya Zama Kakakin Majalisar Wakilai'

Gwamna Mai Mala Buni ya ce lokaci ya yi da APC zata saka wa mataimakin kakakin majalisar wakillan tarayya, Ahmed Idris Wase.

Buni ya ce Wase ya yi wa jam'iyya biyayya a baya lokacin da aka nemi ya janye, don haka ya zama dole yanzu a janye masa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel