Zaben Cike Gurbi: PDP Ta Ce Lallai Sai Dai INEC Ta Tsige Kwamshinan Zabe Na Adamawa

Zaben Cike Gurbi: PDP Ta Ce Lallai Sai Dai INEC Ta Tsige Kwamshinan Zabe Na Adamawa

  • Jam'iyyar PDP ta nemi hukumar zabe da ta tsige Mallam Hudu Yunusa Ari a matsayin kwamishinan zaben jihar Adamawa
  • PDP na zargin Mallam Ari da nuna son kai tare da kokarin murde sakamakon zaben gwamnan Adamawa don nasarar Sanata Aisha Binani ta APC
  • Babbar jam'iyyar adawar kasar ta sake gabatar da wannan bukata a ranar Talata, 4 ga watan Afrilu a Abuja

Abuja - Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta yi kira ga hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) da ta gaggauta tsige kwamishinan zabe na jihar Adamawa, Mallam Hudu Yunusa Ari daga kujerarsa kafin zaben cike gurbi da za a yi a ranar 15 ga watan Afrilu.

Da yake jawabi ga taron manema labarai a hedkwatar jam'iyyar da ke Abuja a ranar Talata, 4 ga watan Afrilu, Debo Ologunagba, sakataren labaran PDP na kasa ya ce jam'iyyar na adawa da ci gaba da kasancewar Mallam Ari a ofis.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 3 da Suka Auka Matsalar Zabe Bayan Yin Fito Na Fito da Buhari a Kan Canjin Kudi

Yan takarar gwamna a zaben Adamawa
Zaben Cike Gurbi: PDP Ta Ce Lallai Sai Dai INEC Ta Tsige Kwamshinan Zabe Na Adamawa Hoto: Gov Umaru Fintiri and Senator Aishatu Dahiru
Asali: Facebook

Ci gaba da kasancewar Ari a matsayin kwamishinan zabe zai ta da zaune tsaye, PDP

Ologunagba ya ce ci gaba da rikon kwamishinan zaben a jihar daidai yake da tunzura jama'a su yi abun da suka ga dama, rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yi bayanin cewa bayanai abun dogaro da PDP ta samu ya nuna cewa:

"Hukumar INEC na son ta da zaune tsaye a jihar Adamawa saboda ci gaba da kasancewar Ari a matsayin kwamishinan zabe na Adamawa duk da zarginsa da ake yi da shirya munakisa don magudi a sakamakon zaben gwamna a jihar, duk da karara ya nuna PDP ce a gaba da halastattun kuri'u 31,299 a zaben."

Zargin magudi a karamar hukumar Fufore

Kakakin na PDP ya bayyana lamarin a matsayin tsokana kuma cewa ba za su yarda INEC ta ci gaba da rikon Yunusa Ari a matsayin wanda zai kammala zaben gwamnan na ranar 15 ga watan Afrilu ba.

Kara karanta wannan

Rikicin siyasa: 'Yan APC da PDP sun kaure da kazamar fada a wata jiha, an harbi wani

Ya kuma yi zargin cewa an jiyo Ari a faifan murya yana umurtan jami'in zabe a karamar hukumar Fufore cewa ya canza sakamakon zaben don nasara ya zama a bangaren yar takarar gwamnan APC, Sanata Aisha Binani, rahoton Vanguard.

Zaben gwamnan Adamawa: Nasara na gareni idan Allah ya yarda, Fintiri

A gefe guda, mun ji a baya cewa dan takarar gwamnan jam'iyyar PDP a jihar Adamawa, Umar Fintiri ya nuna karfin gwiwar cewa shine zai yi nasara a zaben gwamna da za a kammala a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel