Gwamnoni APC Sun Dau Dumi, Sun Ba DSS Wani Zazzafan Umurni

Gwamnoni APC Sun Dau Dumi, Sun Ba DSS Wani Zazzafan Umurni

  • Gwamnonin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) sun buƙaci DSS tayi ram da masu shirin kafa gwamnatin wucin gadi
  • Gwamnonin sun ce waɗannan ɓata garin sun cancanci tuhuma saboda basu son cigaban ƙasar nan
  • Gwamnonin na APC sun yi nuna kan hanyoyin da doka ta tanada kan waɗanda suke ganin ba ayi musu adalci ba a zaɓe

Abuja- Gwamnonin jam'iyyar All Progressives Congress (APC), sun buƙaci rundunar tsaron farin kaya (DSS) da ta cafke sannan ta tuhumi waɗanda ke shirin kafa gwamnatin wucin gadi a ƙasar nan. Rahoton The Cable

A ranar rundunar tsaron farin kayan ta bayyana cewanta bankafo shirin wasu mutane na kafa gwamnatin wucin gadi domin hana rantsar da Bola Tinubu a matsayin shugaban ƙasa. Rahoton Arise News

Gwamnoni
Gwamnoni APC Sun Dau Dumi, Sun Ba DSS Wani Zazzafan Umurni Hoto: The Cable
Asali: UGC

A wata sanarwa ranar Juma'a, gwamnan jihar Kebbi kuma shugaban gwamnonin APC, Atiku Bagudu, ya bayyana cewa abin takaici ne wasu masu son kan su suna son su gurɓata cigaban da dimokuraɗiyyar ƙasar nan ta samu.

"Bayan an fafata a zaɓe, jam'iyyu suna da ƴancin zuwa kotu domin neman haƙƙin su." A cewar Bagudu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Tabbas, kowa yasan cewa jam'iyyun PDP da LP sun zaɓi da suje gaban kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa domin ƙalubalantar sakamakon zaɓen shugaban ƙasa wanda Asiwaju Bola Ahmed Tinubu APC ya lashe.
“A dukkanin jihohin ƙasar nan an kafa kotuna domin bayar da dama ga waɗanda suka yi takara a zaɓen kuma basu gamsu ba, su ƙalubalanci sakamakon."
"Muna kira ga ƴan Najeriya da su mayar da hankali sannan su yi baya da duk wani irin abu da ka iya kawo naƙasu ga dimokuraɗiyyar mu."
“Ƙasar mu tayi ƙoƙari sosai wajen tallata dimokuraɗiyya a cikin gida da ƙasashen Afrika, sannan akwai takaici ace wasu marasa kishin ƙasa suna ƙulla shirin kafa gwamnatin wucin gadi wacce zata rusa dimokuraɗiyyar mu."

Tinubu Ya Rubuta Wa NBC Takarda, Yana Son A Hukunta Channels TV, Ya Bada Dalili

A wani labarin na daban kuma, Tinubu ya kai koke a gaban NBC kan Peter Obi da mataimakin sa Datti Baba-Ahmed.

Tinubu yana zargin su da saɓa dokokin hukumar ta NBC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel