"Makarkashiyar Hana Rantsar Da Tinubu Hadari Ce Babbba", Malamin Musulunci

"Makarkashiyar Hana Rantsar Da Tinubu Hadari Ce Babbba", Malamin Musulunci

  • Wani malamin addinin musulunci yayi tsokaci kan masu ƙoƙarin kawo cikas ga rantsar da Bola Tinubu a matsayin shugaban ƙasa
  • Malamin addinin ya bayyana cewa haɗari ne babba ga Najeriya wannan maƙarƙashiya da suke ƙullawa
  • Sheikh Abdulrahman Ahmad ya kuma yi kira ga musulmai da su taimakawa marasa ƙarfi a cikin watan Azumin Ramadan

Jihar Legas- Jagoran ƙungiyar Ansar-Ud-Deen Society of Nigeria, Sheikh AbdurRahman Ahmad, ya bayyana ƙoƙarin da ake yi na kawo cikas kan rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu, a ranar 29 ga watan Mayun 2023, a matsayin abu mai haɗarin gaske. Rahoton Punch

Tun da farko kakakin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Festus Keyamo, yayi zargin akwai masu son kitsa maƙarƙashiya domin kawo cikas ga miƙa mulkin. Rahoton New Telegraph

Kara karanta wannan

Asiri Ya Tonu: Babban Abinda Ya Sa Abba Gida-Gida Ya Lallasa APC a Zaben Gwamna a Kano

Sheikh Ahmad
"Makarkashiyar Hana Rantsar Da Tinubu Hadari Ce Babbba", Malamin Musulunci Hoto: Muslim News Nigeria
Asali: UGC

A yayin da yake jawabi a wajen lakcar shekara-shekara ta watan Ramadan wacce Ansar-Ud-Deen Society of Nigeria ta shirya a birnin Legas, ranar Lahadi, malamin addinin yace wannan shirin zai kawo rashin haɗin kai a ƙasar.

A kalamansa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Rashin dabara ne babba wani yayi tunanin zai iya amfani da hanyoyin da basa kan doka ya kawo cikas kan wannan rantsuwar. Hakan haɗari ne babba saboda yana da muhimmanci wajen haɗin kan ƙasa."
Sannan kuma yana da muhimmanci wajen jindaɗin al'ummar ƙasar nan. Idan har muna son ƙasar mu, dole ne mu yi rayuwa tare da kundin tsarin mulki."
"Sannan idan akayi zaɓe kuma ba a soke shi a hukumance ba, dole ne a rantsar da wanda ya samu nasara. Waɗanda suke tunanin kawo cikas akai yakamata su sake tunani domin kansu da Najeriya da kuma ƴan Najeriya."

Kara karanta wannan

Matashiya: Yadda Jami'ar Chicago ta Tabbatar da Cewa Makarantar Tinubu Ya Halarta

Sheikh Ahmad, wanda yayi magana a wajen lakcar mai taken "Zuwa ga cikakkiyar nasara" ya bayyana lokacin Azumin Ramadan a matsayin lokacin rahama wanda yakamata musulmai su taimakawa marasa ƙarfi daga cikin su.

“Mutane na shan wahala sosai a ƙasar nan. Babu abinci babu kuɗi. Saboda haka yakamata musulmai su taimakawa marasa ƙarfi da abinci domin su samu su yi ɓuɗa baki cikin natsuwa."

Gwamnan APC Ya Samu Hujjojin Yadda Aka Yi Amfani da Sojoji Wajen Hana Shi Zarcewa

A wani labarin na daban kuma, gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya bayyana yadda akayi amfani da ƙarfin soji wajen kawowa tazarcen sa cikas.

Gwamnan na jam'iyyar APC, bai samu nasara ba a tazarcen da ya nema.

Asali: Legit.ng

Online view pixel