Peter Obi, Datti: Tinubu Ya Rubuta Wa NBC Takarda, Yana Son A Hukunta Channels TV, Ya Bada Dalili

Peter Obi, Datti: Tinubu Ya Rubuta Wa NBC Takarda, Yana Son A Hukunta Channels TV, Ya Bada Dalili

  • Hukumar kula da kafafen watsa labarai na Najeriya, NBC, ta samu sabon korafi daga zababben shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
  • Hakan na zuwa ne yayin da Tinubu ya yi korafi yana neman a hukunta Channels Television kan zargin saba dokar aiki na NBC
  • A cewar zababben shugaban kasar, Channels TV ta kyalle bakonta, dan takarara mataimakin shugaban kasa na LP, Datti Baba-Ahmed, ya furta maganganu da ka iya tada tsaye

Zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu, ya rubuta takardan korafi zuwa ga Hukumar kula da kafafen watsa labarai na kasa, NBC, yana bukatar da hukunta Channels Television kan zargin saba dokokin NBC.

A takarar korafin, mai dauke da kwanan wata na 20 ga watan Maris, Tinubu ya yi kira ga hukumar ta hukunta Channels Television kan zargin saba dokar NBC, Vanguard ta rahoto a ranar Juma'a 31 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Bayanai Sun Fito Yayin Da Shettima Ya Gana Da IBB, Abdusalami Gabanin Rantsar Da Tinubu

Bola Tinubu
Bola Tinubu na son NBC ta hukunta Channels TV saboda kyalle Datti furta maganganu da suka saba doka Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Abin da ya sa ya kamata a hukunta Channels TV, Tinubu ya magantu

Tsohon gwamnan na jihar Legas ya zargi Baba-Ahmed da furta maganganu na sukar nagartar zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu.

A hirar, Datti ya soki nasarar Tinubu a matsayin zababben shugaban kasa kuma kai tsaye ya bukaci Shugaba Buhari da Alkalin Alkalai na kasa kada su rantsar da shi.

A takardar korafinsa, Tinubu ya ce ya kamata mai gabatar da shirin ya ja kunnen dan takarar na Labour kan furta irin wannan maganganun kuma saboda rashin yin hakan, ya kamata a hukunta gidan talabijin din.

APC ta yi martani kan neman izinin yin zanga-zanga da jam'iyyar Labour ta yi a White House

A bangare guda, jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a Amurka ta soki zanga-zanga da jam'iyyar Labour ke shirin yi a White House.

Kara karanta wannan

Sakamakon Zaben Shugaban Kasa Na 2023: Jigon APC Ya Ce Peter Obi Ba Zai Yi Nasara A Kotu Ba, Ya Bada Dalili

Amurka ta bada izinin magoya bayan dan takarar shugaban kasa na LP Peter Obi su yi zanga-zanga a wani filin shakatawa da ke kusa da White House a ranar Litinin 3 ga watan Afrilu.

An tattarro cewa jami'ai a Amurka za su bari a yi zanga-zangan amma mutane 100 kawai za a bari su halarci zanga-zangan kuma na yan awanni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel