Ana Saura Wata 2 Cikar Wa'adin Mulkin Sa, Wani Babban Ministan Buhari Yayi Murabus

Ana Saura Wata 2 Cikar Wa'adin Mulkin Sa, Wani Babban Ministan Buhari Yayi Murabus

  • Minista a ministiri mai gwaɓi a gwamnatin shugaba Buhari, Timipre Sylva, yayi murabus daga muƙamin sa
  • Ƙaramin ministan na albarkatun man fetur yayi murabus ɗin ne a ranar Juma'a domin tsunduma cikin harkokin siyasa
  • Majiyoyi sun tabbatar da cewa ministan yayi murabus ne domin tsayawa takarar gwamnan jihar Bayelsa a inuwar jam'iyyar APC

Abuja- Ƙaramin ministan albarkatun man fetur, Cif Timipre Sylva, yayi murabus daga muƙamin sa.

Bayanan da kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) ya samo a birnin tarayya Abuja a ranar Juma'a daga hannun majiyoyin da ba a gama tabbatar da su ba, sun ce ministan ya miƙa takardar ajiye aikin sa ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari. Rahoton The Guardian

Sylva
Ana Saura Wata 2 Cikar Wa'adin Mulkin Sa, Wani Babban Ministan Buhari Yayi Murabus Hoto: The Guardian
Asali: UGC

A cewar majiyoyin Timipre Sylva yana da niyyar tsayawa takarar gwamnan jihar Bayelsa a zaɓen fidda gwani na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) wanda akwai yiwuwar za a gudanar da shi a watan Afrilu mai zuwa.

Kara karanta wannan

Zabaɓben Gwamnan APC a Jihar Sakkwato Ya Roki Tambuwal, PDP da Wasu Mutane Abu 1

Sylva ya taɓa mulkin jihar Bayelsa sau ɗaya a baya, sannan kundin tsarin dokar ƙasar nan ya bashi damar sake neman kujerar gwamnan jihar a karo na biyu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A halin da ake ciki, da aka tuntuɓi mai babban mai taimakawa ministan kan harkokin watsa labarai, Horatius Egua, yace ba zai iya musanta ko tabbatar da hakan ba domin bai da masaniya akan lamarin. Rahoton PM News

Horatius ya bayyana cewa bai yi ido huɗu da takardar murabus ɗin ba sannan ministan bai gaya masa a hukumance cewa yayi murabus ba.

Sai dai binciken da Legit Hausa tayi, ta samo cewa tabbas ministan yayi murabus daga muƙamin sa. Ta samo hakan ne a wajen hadimin shugaban ƙasa, Bashir Ahmad.

Bashir Ahmad a wani rubutu da yayi a shafin sa na Twitter ya tabbatar da cewa ministan yayi murabus daga muƙamin sa. Kuma yayi murabus ɗin ne domin ya tsaya takarar gwamnan jihar Bayelsa.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Ƴan Shi'a Sun Dirar wa Abuja, Suna Nema A Bawa El-Zakzaky Fasfo ɗin sa

Watanni 2 Kafin Ya Bar Ofis, ‘Yan Majalisa Sun Amince da Bukatar da Buhari Ya Kawo

A wani labarin na daban kuma, majalisar wakilan tarayya ta Najeriya ta amince da wani ƙudirin da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya aike zuwa gabanta.

Hakan na zuwa ne ana saura ƙiris shugaban yayi bankwana daga kan kujerar mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel