Zaben Shugaban Kasa Na 2023: Atiku Ya Yi Magana Kan Janye Kararsa Na Kallubalantar Nasarar Bola Tinubu

Zaben Shugaban Kasa Na 2023: Atiku Ya Yi Magana Kan Janye Kararsa Na Kallubalantar Nasarar Bola Tinubu

  • Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya musanta cewa zai janye kararsa kan sakamakon zaben ranar 25 ga watan Fabrairu
  • Atiku, tsohon shugaban kasa, ya nisanta kansa daga sanarwar manema labarai da aka fitar kan hakan, yana mai cewa na bogi ne
  • Dan takarar shugaban kasar na PDP ya ce an yi magudin zabe a wurare da dama kuma lauyoyinsa har yanzu suna aiki don kallubalantar zaben a kotu

FCT, Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya musanta cewa ya janye karar da ya shigar na kallubalantar nasarar zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya wallafa a sahihin shafinsa na Facebook a ranar Asabar, 25 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: "Abin Da Yan Adawa Suka Shirya Yi Yayin Rantsar Da Ni", Tinubu Ya Yi Fallasa, Ya Ambaci Sunaye

Atiku
Atiku yayin da ake tantance shi da na'urar Bvas kafin ya yi zabe. Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce an fitar da sanarwar manema labarai ta bogi, da ke ikirarin cewa ya amince da sakamakon zaben shugaban kasa na 2023 wanda ya bayyana a matsayin 'zaben da aka yi magudi sosai.'

Zaben shugaban kasa na 2023: Zan kallubalanci nasarar Tinubu - Atiku ya jadadda

Bayan karyata sanarwar manema labaran, Atiku ya kuma jadadda cewa har yanzu yana kotu don kallubalantar sakamakon zaben shugaban kasar na 2023.

Ya ce:

"Don kawar da waswasi, ina son in bayyana cewa har yanzu lauyoyi na suna da cikakken izini daga gare ni don cigaba da kallubalantar sakamakon zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu.
"Ina tare da sauran masoya dimokradiyya a Najeriya da abokan kasarmu wurin kin amincewa da sakamakon zaben na ranar 25 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kotun Daukaka Kara Ta Yanke Hukunci Kan Karar Da PDP Ta Shigar Kan Soke Takarar Tinubu Da Shettima

"Zan cigaba da kallubalantar halascin zaben tare da jam'iyya ta, jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP."

Martanin wasu yan Najeriya kan maganan Atiku

Yahya Idris ya ce:

"Muna da kwarin gwiwa kuma muna addu'a cewa za mu kwato nasarar mu da izinin Allah."

Usman Ahmed ya ce:

"Ranka ya dade, gwagwarmayarka na dimokradiyya a Najeriya baya wuce lokacin zabe kawai ra'ayin kanka ka ke yi wa fafutikan, ba don yan Najeriya ka ke yi ba."

Yusuf Alhaji Mudi cewa ya yi:

"Wannan jagora ne na gaskiya, kuma wanda ya yarda da dimokradiyya, Ranka ya dade, yan Najeriya na alfahari da kai."

Ba mu yarda da zaben ba, za mu tafi kotu: Martanin PDP kan zaben gwamnan Katsina

A wani labari mai kama da wannan, jam'iyyar PDP reshen jihar Katsina ita ma ta ce ba ta amince da sakamakon zaben gwamna da aka yi a ranar 18 ga watan Maris a jihar ba.

Kara karanta wannan

Wike Ya Dauki Zafi a Kan Peter Obi, Ya Bayyana Zunuban Dan Takarar Shugaban Kasar Na LP

Kamar yadda Mustapha Inuwa, shugaban kwamitin kamfe na Atiku/Lado ya bayyanawa manema labarai, ya ce za su tafi kotu don kallubalantar zaben.

Asali: Legit.ng

Online view pixel