Zaben 2023: "Abin Da Yan Adawa Suka Shirya Yi Yayin Rantsar Da Ni", Tinubu Ya Yi Fallasa, Ya Ambaci Sunaye

Zaben 2023: "Abin Da Yan Adawa Suka Shirya Yi Yayin Rantsar Da Ni", Tinubu Ya Yi Fallasa, Ya Ambaci Sunaye

Zababben shugaban kasa Asiwaju Bola Tinubu ya yi jan hankali kan tuggu da wasu yan adawa masu fushi da nasararsa ke kullawa don kawo cikasa ga mika mulki musamman a ranar 29 ga watan Mayu da za a rantsar da shi.

Tinubu ya kuma gargadi yan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, da takwararsa na jam'iyyar Labour, Peter Obi, kan yin zanga-zanga a titi yayin da suka shigar da kara a kotu, Vanguard ta rahoto.

Bola Tinubu
Zaben 2023: "Abin Da Yan Adawa Suka Shirya Yi Yayin Rantsar Da Ni", Tinubu Ya Yi Fallasa, Ya Ambaci Sunaye
Asali: Facebook

A wani sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, 25 ga watan Maris, Direktan harkokin watsa labaransa, Festus Keyamo, Tinubu ya ce wadanda ke son yin zanga-zanga ne son ganin ya kafa gwamnatin hadin gwiwa ne.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Yadda Aka Min Tayin N100m Don In Janye Takara, Dan Shekaru 33 Da Ya Kayar Da Kakakin Majalisar Yobe

Wani sashi na sanarwar ta ce:

"Muna lura kuma da damuwa kan irin ayyukan da wasu mutane da kungiyoyi ke yi na neman murkushe dimokaradiyyar mu.
"Bisa dalilai da sune kadai suka sani, wadannan mutanen suna cike da bakin ciki tun bayan ayyana Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya lashe babban zaben 2023. Sau da yawa, wadannan mutanen marasa alkibla sun sha nanata kiran cewa a soke zabe ko kuma kada a rantsar da zababben shugaban kasar a ranar 29 ga watan Mayu.
"Muna son jadada cewa wannan matakan sun ci karo da kundin tsarin mulkin mu da dokokin zabe. Mun dauki abin matsayin shaci-fadi amma saboda tasirin da za su iya yi kan tsaron kasa da oda, mun ga cewa ya zama dole a jawo hankalinsu.
"Muna sane da niyyar wadanda ke neman aikata laifin cin amanar kasa. Mun kuma san wadanda ke da hannu a wannan sharin da ake kullawa don kawo cikas ga mika mulki da dimokradiyya baki daya. Sun sanya idonsu kan gwamnatin hadin gwiwa. Sun taba yin hakan a baya sun jefa kasar cikin rikici kuma suna son sake yin hakan. Sun dage sai sun haramta sabuwar gwamnatin. Wasu sun bayyana maganganu na cin amanar kasa a fili na kira sojoji su kwace mulki. Don wannan dalilan ne ya sa suke son tunzura al'umma su bijire wa gwamnati."

Kara karanta wannan

Zabe: Dalilin Da Yasa Shugabannin Najeriya Da Ke Kan Mulki Ke Shan Kaye A Akwatunan Aso Rock

Sanarwar ta cigaba da cewa:

"Abin mamaki ne ganin cewa wadanda ke kalubalantar sakamakon suna so su kasance a kotu da kan tituna a lokaci guda. Duk da haka, idan niyyarsu ita ce ta dakile rantsar da zababben shugaban kasa da mataimakinsa, ya kamata su binne wannan tunanin. Abin farin ciki ne ganin cewa shugaban kasar ya fara shirin mika mulki da da rantsuwarwa. Bisa hakan, kwamitin rikon kwarya na shugaban kasa ya ci gaba da mayar da hankali da kuma jajircewa wajen aiwatar da aikinsa na ganin a mulki ba tare da wata matsala ba.
"Bayan ayyana su a matsayin wadanda suka yi nasara, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da Sanata Kashim Shettima sun cancanci a rantsar da su kamar yadda doka ta tanada kuma muke yi tun 1999, yayin da wadanda ke jin akasin haka suna da damar neman hakkinsu a kotu. Me ya sa a karonsu abin zai bambanta da na yadda muke yi tun shekara ta 1999?

Kara karanta wannan

Ku Tallafawa Mahaifina, Ba Zai Iya Shi Kadai Ba, Yar Tinubu Ta Roki Yan Najeriya

"Abin da kawai muke so shine a samu zaman lafiya a kasar. Ba shi da ma'ana cewa wasu mutane da ya kamata su san abin da ya dace su goyon bayan tashin hankali ba kuma sun dage don cimma hakan.
"Mun san wadannan mutane da masu daukar nauyin su daga ciki da wajen Najeriya kuma za mu yi aiki kafada da kafada da hukumomin tsaro don kama su da kuma hukunta su. Abun damuwarmu shi ne kada a yi amfani da talakawan Najeriya da ba su san muguntar wadannan mutane ba. Ya isa ya isa. Ya kamata su daina tsayayya da mu nan take. Ba wai ba mu san abin da za mu yi bane. Bai kamata a dauki yin shiru a matsayin tsoro ba. Ya kamata mu hada kai domin zaman lafiya na kasarmu. Hakan ya fi dacewa."

Peter Obi ya gamu da Obasanjo a filin tashin jiragen saman Anambra

Kara karanta wannan

Jerin Abubuwa 5 Da Obi Ya Bukaci Kotun Zabe Ta Yi Masa A Yayin Da Ya Ke Kallubalantar Nasarar Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu, ya gana da Olusegun Obasanjo, tsohon shugaban kasar Najeriya a garin Awka, babban birnin jihar Anambra.

Asali: Legit.ng

Online view pixel