Zaben Gwamnan Katsina: PDP Ta Bayyana Matakin Da Za Ta Dauka Bayan Shan Kaye

Zaben Gwamnan Katsina: PDP Ta Bayyana Matakin Da Za Ta Dauka Bayan Shan Kaye

  • Jam'iyyar PDP ta bayyana rashin amincewarta da salon yadda aka gudanar da zabe gaba daya a Jihar Katsina
  • Daraktan yakin neman zaben Atiku/Lado ne ya bayyana haka yayin hira da manema labarai ranar Litinin a Katsina, in da ya ce za su kalubalanci hakan a gaban kotu
  • PDP ta kuma yi zargin an hana mambobinta kada kuri'a musamman a yankunan da su ke da mafi rinjayen goyon baya

Jihar Katsina - Jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP ta yi watsi da sakamakon zaben gwamnan Jihar Katsina, ta ce za ta garzaya gaban kotu, rahoton The Nigerian Tribune.

Babban daraktan kwamitin yakin neman zaben Atiku/Lado, Dakta Mustapha Inuwa ne ya sanar da matsayar jam'iyyar a hira da manema labarai ranar Litinin a Katsina.

Jam'iyyar PDP
Jam'iyyar PDP Za Ta Tafi Kotu Kan Zaben Gwamnan Jihar Katsina. Hoto: The Nation
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

Yanzu Haka: Kwankwaso Da Buba Galadima Sun Dira Ofishin INEC A Kano Yayin Da Ake Jiran Sakamako Zabe

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa an bayyana dan takarar jam'iyyar APC, Dr Dikko Radda ne ya lashe zaben gwamnan jihar da kuri'a 859,892.

Ya kayar da dan takarar jam'iyyar PDP, Yakubu Lado-Danmarke, wanda ya samu kuri'a 486,620.

Sakamakon zaben ya sha banban da yadda jama'a suka fito, Lado-Danmarke

A cewar Inuwa, sakamakon ya saba da yadda jama'a su ka fito a ranar Asabar.

Ya cigaba da cewa:

''Ba a yi zabe ba a jihar. Mu na so mu sanar da ku ba tare da boye boye ba cewa mun yi Allah wadai kuma mun yi watsi da sakamakon zaben da aka gudanar ranar Asabar, 18 ga watan Maris, 2023.
''An samu tashin hankali, bata suna, tilastawa, kyara da duk wani nau'i na magudi.''

Ya kuma yi ikirarin cewa an hana magoya bayan PDP kada kuri'a musamman a wuraren da su ke da karfi sosai.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnan APC Ya Sha Da Ƙyar, Ya Lashe Zaben Gwamna a Jiharsa

''To, ina so in sanar da ku cewa ba mu amince ba kuma mu na Allah wadai, kuma za mu tafi kotu don kalubalantar gaba daya zaben.''

Masu kada kuri'a sun ki karbar tiransifa ta kudi a a jihar Niger

A wani rahoton, kun ji cewa wasu cikin wadanda suka tafi yin zabe a karamar hukumar Tafa da ke jihar Neja sun ki yarda da alkawarin a yi musu tiransifa na kudi daga wakilan jam'iyyu, suka ce sun gwammace a ba su abinci kafin su yi zaben a ranar Asabar da ta gabata.

Masu zaben sun ce sun san karbar kudi daga hannun yan siyasa yayin zabe laifi ne amma ita ce hanyar kadai da suke morar su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel