Majalisar Dokokin Jihar Ƙogi Ta Dakatar Yan Majalisu 9 da Ciyamomi 5

Majalisar Dokokin Jihar Ƙogi Ta Dakatar Yan Majalisu 9 da Ciyamomi 5

  • Majalisar dokokin jihar Kogi ta dakatar da mambobinta 9 bisa zargin hannu a aikata ta'addanci
  • Bayan haka ta kuma dakatar da shugabannin kananan hukumomi 8 bisa tuhuma guda biyu
  • Ta kafa kwamishin mutane 7 karkashin mataimakin kakakin majalisa domin gudanar da bincike

Kogi - Majalisar dokokin jihar Kogi ta dakatar da 'yan majalisar jiha guda 9 da kuma shugabannin kananan hukumomi Bakwai, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Ta ɗauki wannan matakin ne bayan kakakin majalisar, Honorabul Mathew Kolawole, ya karanta wasiƙar gwamna Yahaya Bello, wanda zargin 'yan majalisu 9 da hannu a aikata ta'addanci.

Zauren majalisar dokokin jihar Kogi.
Majalisar Dokokin Jihar Ƙogi Ta Dakatar Yan Majalisu 9 da Ciyamomi 5 Hoto: leadership
Asali: UGC

Da yake faɗin ra'ayinsa kan zargin da ake wa mambobin guda 9, mataimakin shugaban majalisar, Alfa Rabiu Momoh, ya goyi bayan a dakatar da su nan take.

Ya ce jihar Kogi ta zarce duk wasu burikan son rai kuma ko kaɗan bai kamata a gano 'yan majalisa masu yin doka amma suna ƙarya doka da oda.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An kama wasu da ke sace yara da sunan za su kaisu gidan marayu a jihar Arewa

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Haka zalika, Honorabul Collins Musa, mai wakiltar mazaɓar Omala, ya bi sahun matsayar mataimakin kakaki, ya ce duk batun da ya haɗa alaka da ta'addanci ya fi ƙarfin a rufe shi.

Bayan muhawara, majalisar ta amince ta dakatar da mambobin guda 9 har zuwa lokacin da aka kammala bincike kan zargin da ake masu.

Jerin mambobin da aka dakatar

Mambobin majalisar da matakin ya shafa sun ƙunshi, Olusola Kilani (Ijumu), Bello Hassan (Ajaokuta), Muhammed Lawi Ahmed (Okene 1), Moses Akande (Ogori Magongo), da Aderonke Aro (Yagba ta arewa).

Sauran su ne, Daniyan Ranyi (Bassa), Atule Igbunu (Ibaji), Atachaji Musa (Idah), da kuma Muktah Bajeh (Okehi).

Majalisa ta dakatar da wasu Coyamomi da mataimakansu

Bayan tattake wuri kan wancan batun, majalisar ta sake ɗaukar matakin dakatarwa kan shugabannin kananan hukumomi 7 kan zargin haddasa rikici a lokacin zaɓe.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Shugaban Masu Rinjaye Na Majalisar Dokokin Jihar APC Ya Yi Murabus Kan Abu 1 Tak

Kananan hukumomin da aka dakatar da shuganninnsu da mataimaka sun haɗa da Bassa, Ogori/Magongo, Yagba ta yamma, Ibaji, Kabba/Bunu, Ajaokuta da kuma Adavi.

Leadership ta rahoto cewa majalisar ta kafa kwamitin mutum Bakwai karkashin jagorancin mataimakin kakaki, wanda zai gudanar da bincike kan ciyamomin guda 7.

Bugu da ƙari, majalisar ta dakatar da shugaban karamar hukumar Lokoja, Dansabe Muhammed, bisa zargin karakartar da wasu kuɗaɗe da suka kai miliyan N150m.

A wani labarin kuma Gwamnatin Kaduna Ta Malam Nasiru El-Rufai Ta Fallasa Shirin Wasu Yan Siyasa Na Haddasa Rikici

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwa, ya ce duk wanda ya sake aka kama shi da hannu a lamarin zai danɗana kuɗarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262