Shugaban Masu Rinjaye Na Majalisar Dokokin Jihar Kogi Ya Yi Murabus

Shugaban Masu Rinjaye Na Majalisar Dokokin Jihar Kogi Ya Yi Murabus

  • Honorabul Muktar Bajeh, ya yi murabus daga muƙamin shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar Kogi
  • Ɗan majalisar mai wakiltar mazabar karamar hukumar Okehi, ya ce ya yi haka ne don maida hankali kan nauyin dake kansa
  • Ya gode wa gwamna Yahaya Bello, shugaban majalisa da kuma baki ɗaya abokan aikinsa bisa damar da suka ba shi

Kogi - Shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar Kogi, Honorabul Muktar Bajeh, ya yi murabus daga kan mukaminsa ranar Alhamis 23 ga watan Maris, 2023.

Ɗan majalisar ya bayyana cewa ya ɗauki matakin sauka daga mauƙamin ne saboda nauye-nauyen da suka hau kansa waɗanda ke bukatar ya maida hankali kansu.

Mukhtar Bajeh.
Tsohon shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin Kogi, Muktar Bajeh Hoto: tribune
Asali: UGC

Matakin murabus ɗin na kunshe ne a wata wasiƙa da Bajeh ya aike wa kakakin majalisar dokokin jihar, Honorabul Matthew Kolawole, mai ɗauke da kwanan watan 20 ga watan Maris, 2023 kuma ya rattaɓa hannu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yanzu: Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Ekweremadu Bisa Zargin Safarar Sassan Jiki

A rahoton Tribune Online, ɗan majalisar ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Bayan dogon tunani mai zurfi tare da nadama, ya zama wajibi na faɗa wa duniya cewa na ɗauki mataki mai wahala na murabus daga mukamin shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar Kogi."

A wasikar da ya aike wa majalisar kuwa, Bajeh ya yaba da alfarmar da ya samu tun daga mukamin mai tsawatarwa zuwa shugaban masu rinjaye.

Wani sashin wasikar murabus ɗin ya ce:

"Na rubuta wannan wasika ne domin sanar maka na sauka daga mukamin shugaban masu rinjaye, ni ke wakiltar mutanen mazaɓar karamar hukumar Okehi."
"Na yi murabus ne saboda nauye-nauyen da ke tunkaro ni waɗanda zasu bukaci maida hankali na cikin gaggawa. Na gode da alfarmar da aka mun tun daga zuwa na, a matsayin mai tsawatarwa yanzu shugaban masu rinjaye."

Kara karanta wannan

Jerin Sunaye: Gwamnan APC Ya Naɗa Sabbin Hadimai 30 Watanni 2 Gabanin Ya Sauka Daga Mulki

"Ina miƙa tsantsar godiyata mara adadi ga abokan aikina a majalisa musamman kakakin majalisa wanda na yi aiki da shi tsawon lokaci. Haka nan ina kara gode wa mai girma gwamna, Yahaya Adoza Bello."

Ba zamu zuba ido a hana mutane zaman lafiya ba - Kaduna

A wani labarin kuna Gwamnatin Kaduna Ta Fallasa Shirin Wasu Yan Siyasa da Ta Da Zaune Tsaye

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, ya ce gwamnatin Kaduna ta samu bayanan sirri kuma tana nan tana bibiyar yanayin.

Ya ce babu wani shafaffe da mai da zasu kyale matukar ya zama sanadin lalata dukiyoyi ko barazana ga rayuwar jama'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel