Gwamnatin Kaduna Ta Fallasa Shirin Wasu Yan Siyasa da Ta Da Zaune Tsaye

Gwamnatin Kaduna Ta Fallasa Shirin Wasu Yan Siyasa da Ta Da Zaune Tsaye

  • Gwamnatin Malam Nasiru El-Rufa'i ta gano shirin wasu yan siyasa na ta da zaune tsaye da sunan zanga-zanga
  • Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, ya gargaɗi iyaye da Sarakuna su dakatar da mutanen da suke ƙarkashinsu
  • Aruwan ya ce babu wanda doka zata kyale matukar ya ba da gudummuwa wajen barazana ga rayuwa da lalata dukiyoyi

Kaduna - Gwamnatin jihar Kaduna ta ankarar da cewa wasu 'yan siyasa na shirin tunzura magoya bayansu su fito zanga-zanga da nufin tayar da rikici tsakanin mutane.

Channels tv ta rahoto cewa kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.

Malam Nasiru El-Rufa'i.
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai Hoto: Governor Kaduna
Asali: UGC

Ya ce gwamnati ta samu rahoton sirri kan wannan shirin wanda ya ƙunshi fantsama kan tituna da sunan zanga-zanga ta yadda zasu jawo karya doka da oda.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Tsohuwa ta rude, ta kone danta, matarsa da jikokinta a wata jiha

"Dogaro da rahotannin, gwamnati ta ci gaba da bibiyar yanayin da haɗin kan hukumomin tsaro. Dole duk wasu mutane ko ƙungiya da suka shiga abinda ya ta da hargitsi, barazana ga rayuwa da lalata kadarori, ba zasu ci bulus ba."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Dole doka ta yi aiki a kan ko waye, dokar haramcin zanga-zanga a tituna na nan daram domin kare ɗaukacin al'umma."
"Muna shawartan iyaye, masu kula da 'ya'ya da sarakunan gargajiya su gargaɗi yaransu kan su kauce wa duk wani mutumi da ya nemi amfani da su wajen ta da zaune tsaye."

Wannan na zuwa ne kwanaki biyu bayan INEC ta ayyana Malam Uba Sani na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar Kaduna, kamar yadda Guardian ta rahoto.

Sani ya samu kuri'u 730,002, wanda suka ba shi damar lallasa babban abokin karawarsa na jam'iyyar PDP, Honorabul Isah Ashiru Kudan, wanda ya tashi da ƙuri'u 719,196.

Kara karanta wannan

2023: Jerin Jihohin da Ba'a Kammala Zaben Gwamna Ba da Waɗanda INEC Ta Dakatar da Tattara Sakamako

Umahi ya yi sabon naɗin mutane 30 a gwamnatinsa

A wani labarin kuma Gwamna Umahi Ya Nada Sabbin Hadimai 30 Watanni 2 Gabanin Ya Sauka Daga Kan Madafun Iko

Gwamnan jihar Ebonyi mai barin gado, David Umahi, ya zakulo mutane 30 ya naɗa su a matsayin mataimaka na musamman da zasu sa ido kan ayyukan gwamnati.

Asali: Legit.ng

Online view pixel