Zulum Ya Lashe Karamar Hukuma Ta Farko Da Tazara Mai Girma

Zulum Ya Lashe Karamar Hukuma Ta Farko Da Tazara Mai Girma

  • Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya yi nasarar lallasa abokan hamayarsa a karamar hukumar Munguno
  • Zulum a zaben da aka gudanar a ranar Asabar 18 ga watan Maris ya samu kuri'u 17,187 yayin da abokin hamyarsa mai biye da shi na PDP ya samu kuri'u 280
  • A halin yanzu ana cigaba da tattara sakamakon zaben daga rumfunan zabe da gunduma-gunduma na sassan jihar Bornon da sauran jihohi da aka yi zaben

Jihar Borno - Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, dan takarar jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a zaben ranar Asabar, ya samu kuri'u mafi rinjaye da aka kada a karamar hukumar Munguno.

Yayin da Zulum ya samu kuri'u 17,187 a jihar, Mohammed Jajari, abokin karawarsa na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ya samu kuri'u 280, ya bashi tazarar kuri'u 16,907.

Zulum
Zulum Ya Lashe Karamar Hukuma Ta Farko Da Tazara Mai Girma. Hoto: The Guardian Nigeria
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yan takarar gwamna na jam'iyyun Labour da New Nigeria Peoples Party, NNPP, ba su samu ko da kuri'a guda ba a karamar hukumar, Daily Trust ta rahoto.

Akwai kananan hukumomi 27 baki daya a jihar ta Borno.

Jimillan adadin masu zabe da aka yi wa rajista: 57,196

Jimillan masu zabe da aka tantance: 17,753

Sakamakon jam'iyyun da ke gaban gaba

Kuri'un da jam'iyyun da ke kan gaba suka samu.

APC: 17187

PDP: 280

LP: 00

NNPP: 00

Jimillan kuri'u masu kyau: 27629

Kuri'u marasa kyau: 232

Jimillan kuri'un da aka kada: 17861

Jam'iyyun NNPP da APC a Jihar Kano sun umurci magoya bayansu su raka kuri'u zuwa cibiyoyin tattara sakamakon zabe

A wani rahoton kun ji cewa ana zaman dar-dar a jihar Kano a yayin da manyan jam'iyyu biyu da ke kan gaba a zaben gwamna wato jam'iyyun APC da NNPP suka bukaci magoya bayansu su raka kuri'u zuwa cibiyoyin tattara sakamakon zabe.

Jam'iyyun sun yi hakan ne da nufin tsare kuri'unsu da kare duk wata yunkuri na yin magudin zabe ko sauya alkalluma kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar New Nigeria People Party, NNPP, kuma uban gidan dan takarar gwamnan NNPP na Kano, Abba Kabir Yusuf, shine ya yi wannan kiran a madadin NNPP yayin da kakakin kwamitin kamfe na gwamna na APC, Muhammad Garba ya yi kiran a madadin jam'iyyarsa da ke mulki a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel