Fargaba Yayin Da APC, NNPP Suka Umurci Magoya Bayansu Su Mamaye Cibiyoyin Tattara Kuri'un Zabe A Kano

Fargaba Yayin Da APC, NNPP Suka Umurci Magoya Bayansu Su Mamaye Cibiyoyin Tattara Kuri'un Zabe A Kano

  • Manyan jam'iyyun siyasa na APC da NNPP sun roki magoya baya da su fita zuwa cibiyoyin tattara sakamakon zabe saboda tsoron magudi
  • Jam'iyyar APC ta sanar da haka ta hannun mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben Gawuna/Garo, Mal Muhammad Garba yayin da jagoran NNPP Sanata Kwankwaso ya yi rokon a madadin NNPP
  • Duk da yawan yan takarar da suka fafata a zaben, ana ganin cewa zaben tsakanin jam'iyyu biyu ne kawai a jihar

Jihar Kano - Jam’iyyar All Progressives Congress, APC da New Nigeria People Party, NNPP a jihar Kano sun bukaci magoya bayansu da su raka kuri'unsu zuwa cibiyoyin tattara sakamakon zabe, rahoton Daily Trust.

Yayin da Rabi’u Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na NNPP, ya yi wannan kiran a madadin jam’iyyarsa, kakakin yakin neman zaben Gawuna/Garo, Malam Muhammad Garba, ya yi kiran ga magoya bayan jam’iyya mai mulki.

Kara karanta wannan

Zaben Gwamnan Katsina: PDP Ta Bayyana Matakin Da Za Ta Dauka Bayan Shan Kaye

Abba da Gawuna
Jam'iyyun APC da NNPP sun umurci magoya bayansu su mamaye cibiyar tattara sakamakon zaben Kano. Hoto: Bashir Ahmad, Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

A wata sanarwa da ya fitar a Kano ranar Asabar, Garba ya ce kiran ya zama dole domin bai wa masu ruwa da tsaki na jam’iyyar damar yin taka-tsan-tsan da zagon kasa ko sauya sakamakon zabe.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hakazalika, Kwankwaso, jagoran tafiyar Kwankwasiyya, ya bukaci daukacin magoya bayan jam’iyyar da su mamaye cibiyoyin domin tabbatar da an kirga kuri’u.

A wani takaitaccen sakon bidiyo, Kwankwaso ya yi ikirarin cewa daga sakamakon da aka tattara ya zuwa yanzu, jam’iyyarsa tana da yakinin lashe zaben gwamnan da aka yi ranar Asabar.

Ya dage cewa dole ne a raka kuri’un daga rumfunan zaben su zuwa wuraren tattara sakamako na mazabu har zuwa jiha.

“Ina godiya ga daukacin magoya bayan Kwankwasiyya da NNPP bisa hadin kan da suka ba mu. Amma kuma ina kira ga ’yan kishin kasa da su tabbatar sun bi tsarin tattara kuri'a har zuwa cibiyoyinsu na RAC, da kananan hukumomi da ma matakin jiha.

Kara karanta wannan

Abba Gida-Gida: Dalilai 6 Da Suka Sa Dan Takarar NNPP Ya Kayar Da APC A Kano

"Muna da rahotannin sirri da ke nuna cewa wasu makiyan jihar nan na kokarin yin amfani da wannan damar don kawo cikas ga lamarin," in ji Kwankwaso.

Daily Trust ta ruwaito cewa an kawo karshen kada kuri’a a mafi yawan rumfunan zabe a fadin jihar, yayin da tuni aka fara kidayar kuri’u da kuma fitar da sakamako.

Duk da cewa akwai jam’iyyu da dama da suka fafata, ana kallon zaben Kano a matsayin tseren doki biyu tsakanin Nasiru Yusuf Gawuna na APC da Abba Kabir Yusuf na NNPP

Bidiyon Kwamishinan Bauchi yana rabon kudi gabanin zaben gwamna

A wani rahoton, kun ji cewa wani bidiyo ya yadu a dandalin sada zumunta inda aka gano wani da aka ce kwamishinan matasa da wasanni na jihar Bauchi, Adamu Manu Soro ne yana rabon kudi gabanin zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel