Dan Shekara 35 Ya Raba Kakakin Majalisar Yobe Da Kujerar Da Ya Ke Kai Shekara 20, Kakakin Filato Ya Sha Kaye

Dan Shekara 35 Ya Raba Kakakin Majalisar Yobe Da Kujerar Da Ya Ke Kai Shekara 20, Kakakin Filato Ya Sha Kaye

Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Yobe, Honarabul Ahmed Mirwa Lawan ya rasa kujerarsa, ya sha kaye hannun Lawan Musa, dan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, mai wakiltar mazabar Nguru II, dan shekara 35.

Baturen zabe na jihar, Dr Habib Muhammad, wanda ya sanar da sakamakon zaben ya ce, Musa ya samu kuri'u 6,648 inda ya kayar da kakakin majalisar na jam'iyyar APC wanda ya samu kuri'u 6,466.

Zababben dan majalisa da kakakin majalisar Yobe
Dan shekara 35 ya kayar da Kakakin Majalisar Yobe. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Ya ce dan takarar jam'iyyar ADC ya samu kuri'u 3,023 yayin da yan takarar NNPP da APM suka samu kuri'u 14 kowannensu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Daily Trust ta tattaro cewa Kakakin Majalisar na Yobe ya kasance a majalisar tun shekarar 2003 da aka zabe shi a matsayin dan majalisa karkashin jam'iyyar All Nigeria Peoples Party (ANPP).

Kara karanta wannan

Zulum Ya Lashe Karamar Hukuma Ta Farko Da Tazara Mai Girma

Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Filato Ya Sha Kaye

A wani yanayi mai kama da na jihar ta Yobe, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Filato, Yakubu Sanda, na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ya rasa damar komawa majalisar, rahoton Channels Television.

Yakubu Sanda
Kakakin majalisun Yobe da Filato sun rasa kujerunsu. Hoto: Channels Television.
Asali: Facebook

Misis Happiness Mathew Akawu, yar takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ce ta kayar da shi a zaben da aka yi a ranar Asabar na mazabar Pengana a jihar.

Yar takarar ta jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 9,926 inda ta kayar da kakakin majalisar wana ya samu kuri'u 7,936. Shi kuma dan takarar jam'iyyar PRP ya samu kuri'u 6,721, dan takarar jam'iyyar Labour ya samu kuri'u 1,028.

Ga sakamakon zaben majalisar dokokin jiha na Pengana:

APC – 7,936

PDP – 9,926

PRP – 6,721

LP – 1,028

Dakaci karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Online view pixel