An Yi Dirama Yayin Da Biri Ya Iso Rumfar Zabe Ya Tarwatsa Masu Kada Kuri'a A Kano

An Yi Dirama Yayin Da Biri Ya Iso Rumfar Zabe Ya Tarwatsa Masu Kada Kuri'a A Kano

  • Wani abu mai kama da dirama ya faru a wata rumfar zabe a karamar hukumar Kiru ta jihar Kano yayin da wani ya taho da dan biri
  • Isowar dan birin da mai shi rumfar zaben yasa wasu da dama sun cika wandunansu da iska sun tarwatse sun bar layin zabe saboda ganin birin
  • Amma daga bani jami'an tsaro da ke rumfar zaben da sauran masu ruwa da tsaki sun bukaci mutumin da ke da birin ya koma gefe, aka ja masa layi

Jihar Kano - An samu hatsaniya a wasu akwatunan zabe a karamar hukumar Kiru na jihar Kano a lokacin da wani biri ya tarwatsa masu zabe.

A cewar rahoton Freedom Radio, mai birin ne ya taho da shi wurin zaben.

Biri a Kano
Biri ya tarwatsa masu zabe a Kano. Hoto: Y Mukhtar
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An Bindige Tsohon Kansila A Kano Har Lahira Kan Sace Akwatin Zabe

Amma, daga bisani, abubuwa sun daidaita bayan jami'an tsaro da wasu sauran masu ruwa da tsaki sun gargadi mai birin, suka fada masa kada ya tsallake wani iyaka da aka masa.

Yunwa ta saka masu zabe sun ce a rika basu abinci a madadin tiransifa

Wasu mutane a wani gari mai suna Garam da ke karkashin karamar hukumar Tafa a jihar Neja sun ki amincewa da alkawarin tura musu kudi ta hanyar tiransifa daga wakilan jam'iyyu.

Masu kada kuri'un sun ce idan ba sun ga kudi ko abinci a kasa ba, ba za su jefa kuri'a ga jam'iyyun da wakilan ke so ba, suna mai cewa a yayin zabukan shugaban kasa an yaudare su an ce za su ga tiransifa amma ba su ga komai ba.

Wasu cikin mutanen sun bayyana cewa sun san karbar toshi daga hannun wakilan jam'iyyu ya saba dokar zabe a kasa amma sunce wannan ce hanya guda da za su iya morar wani abu daga yan siyasan shi yasa suka dage.

Asali: Legit.ng

Online view pixel