Bidiyon Yadda Jam’iyyar APC Ta Tafi da Imanin Matar Aure da Kaza a Jihar Kaduna

Bidiyon Yadda Jam’iyyar APC Ta Tafi da Imanin Matar Aure da Kaza a Jihar Kaduna

  • An ga magoya bayan Jam’iyyar APC a Kaduna su na yawon rabawa mutane kayan abinci
  • Wata mata da ta karbi kaza, ta tabbatar da cewa Uba Sani za ta ba kuri’a ya zama Gwamna
  • Sanata Uba Sani yana neman takarar Gwamnan jihar Kaduna a karkashin jam’iyyar APC

Kaduna - Wani bidiyo yana yawo da aka ga magoya bayan jam’iyyar APC a jihar Kaduna, sun yi nasarar samun goyon baya saboda kaza.

Wata Baiwar Allah da aka ba kyautar kaza a Kaduna, ta nuna cewa babu shakka kuri’arta ta na wajen ‘dan takaran APC, Sanata Uba Sani.

A cewar wannan Baiwar Allah, da farko ba ta da niyyar yin zabe, amma yanzu za ta kadawa jam’iyya mai mulki ne a zaben sabon Gwamna.

Bisa dukkan alamu wannan mata da aka gani cikin dogon lullubi matar aure ce domin za a iya ganin kananan yara biyu a cikin bidiyon.

Kara karanta wannan

Gaskiyar Magana Ta Fito, Ta Tabbata INEC ta ba ‘Yar Takarar APC Kwangilar Kayan Zabe

Kaza ta ba Uba Sani kuri'a

Matan da ke kamfe sun mikawa matar kaza, ita kuwa ta zuba a kwano ta rika shararo addu’a. Northernblog suka fitar da bidiyon a Twitter.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Uba Sani
Sanata Uba Sani da kaza Hoto: www.epicurious.com/UbaSani
Asali: UGC

‘Yar APC: Me ki ke bukata a cikin kayan da aka kawo? Akwai kwai, akwai indomie, akwai kaza?

Matar gida: Wallahi ni kaza na ke bukata.

‘Yar APC: Kaza ki ke bukata?

Matar gida: Kaza na ke bukata in dangwalawa Uba Sani. Yadda Allah ya kawo mu wannan lokaci, ya taya shi riko, ya kara masa daukaka. Allah ya saka da alheri.

Ban da niyyar dangwala masa amma tun da zan dangwali kaza, Allah ya sa ya fi haka, Allah ya shige masa gaba, Allah ya saka da alheri.

Mutane sun ce wani abu

Kara karanta wannan

Allura Na Kokarin Tona Garma a Zargin Cinye N500m Na Kamfe a Jam’iyyar APC

Mutane sun tofa albarkacinsa a game da wannan bidiyo, ana zargin wannan mata da saida ‘yancinta a kan abin da bai kai ya kawo ba.

Aliyu Kwarbai matashi ne da yake goyon bayan PDP a Kaduna, ya ce an soki tsarinsu na raba awaki, APC ta buge da kyautan tumaki.

Imam Anas yake cewa

“Abin takaici ne iyayenmu su na saida makomarmu saboda kaza.”
“Za a ci yaki a Kaduna da budurwar kaza.”

- Inji King Bash 47

INEC ta ba Binani kwangila

An ji labari INEC ta bada kwangilar buga takardun sakamakon zaben Gwamnoni ga ‘yar takarar APC a jihar Adamawa a zaben bana, Aishatu Dahiru Binani.

Kamfanin Aishatu Dahiru Binani wanda take neman Gwamnan jihar Adamawa ya buga takardun Jigawa, Kaduna, Kebbi, Kaduna, Kano, Zamfara da Sokoto.

Kara karanta wannan

Asiri Zai Tonu, Shugabannin Jam’iyyar APC Na Fada Kan Zargin Cinye Kudin Kamfe

Asali: Legit.ng

Online view pixel