Gaskiyar Magana Ta Fito, Ta Tabbata INEC ta ba ‘Yar Takarar APC Kwangilar Kayan Zabe

Gaskiyar Magana Ta Fito, Ta Tabbata INEC ta ba ‘Yar Takarar APC Kwangilar Kayan Zabe

  • Hukumar INEC mai zaman kan ta, ta ba Binani Printing Press Limited kwangila a zaben 2023
  • Abin ban mamaki shi ne ‘Yar takarar APC ce ta ke da kamfanin na Binani Printing Press Limited
  • Sai dai INEC ta ce ba ta san kamfanin yana da wata alaka da Sanata Aishatu Dahiru Binani ba

Abuja - Hukumar INEC mai shirya zabe a Najeriya ta tabbatar da ta bada kwangilar buga kayan zabe ne ga kamfanin Binani Printing Press Limited.

Bayan rahoto ya fito daga Sahara Reporters cewa ‘yar takarar jam’iyyar APC ta samu kwangila daga INEC, a makon nan hukumar kasar ta yi karin haske.

Daily Trust ta rahoto cewa kamfanin Sanata Aishatu Dahiru Binani ya samu kwangila daga INEC domin buga takardun sakamakon zaben Gwamna.

Binani Printing Press Limited ya buga takardun da za ayi amfani da su a 2023 a Jihohin Jigawa, Kaduna, Kebbi, Kaduna, Kano, Zamfara da Sokoto.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP Ya Tsorata Kafin Ranar Zabe, Ya Kai Karar ‘Dan Takaran APC Wajen Buhari

'Yar takara ta zama 'Yar kwangila

Yanzu haka Aishatu Dahiru Binani tana wakiltar Adamawa ta tsakiya a majalisar dattawa na kasa kuma ta na neman takarar Gwamna a jam’iyyar APC.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hukumar INEC ta ce baro-baro aka tallata kwangilar, kuma wannan kamfani ya yi dace aka ba shi, ba tare da sanin alakarsa da ‘yar takarar Gwamnan ba.

Kamfen APC
Kamfen Aishatu Dahiru Binani Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Ya aka yi INEC ba ta lura ba?

INEC ta nuna cewa babu ‘Aishatu Dahiru Ahmed’ a cikin sunayen Darektocin wannan kamfani, don haka ba a duhu ta ba kamfanin kwangila.

Jaridar ta rahoto cewa bincike ya nuna mata sunan ‘Aisha Dahiru’ yana cikin Darekocin Binani Printing Press Limited da INEC ta ba kwangilar nan.

Dayar Darektar kamfanin ita ce Hauwa Dahiru (watakila ‘yaruwar 'yar takarar ce) sai kuma Gamzaki Gamzaki Law Chamber a matsayin Sakatare.

Kara karanta wannan

Na boye ya ya bayyana: Jigon APC ya yi sakin baki, ya fadi dalilin nasarar Bola Tinubu

Premium Times ta ce Kwamishinan yada labarai da wayar da kan masu zabe na INEC, Festus Okoye ya yi wanan kari haske a yammacin Alhamis.

Festus Okoye ya ce sun yi bincike a hukumar CAC, kuma sun gamsu cewa wannan kamfani ya kware wajen buga takardu, sannan a yaba da tsaronsu.

Shugaban APC ya fadawa Sakatare ya fito da kudin kamfe

Shugaban APC na shiyyar Arewa maso yamma ya cigaba da fallasa Sakataren jam’iyya na kasa, an ji labari ya yi wa Sanata Iyiola Omisore raddi.

Dr. Salihu Lukman ya ce Omisore ne wanda ya jawowa Atiku Abubakar ya doke Bola Tinubu a Osun domin ya lakume kudin yakin zaben APC a jiharsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel