Yan Daba Sun Far Wa Tawagar Kamfe Na Dan Takarar Jam'iyyar Labour A Legas

Yan Daba Sun Far Wa Tawagar Kamfe Na Dan Takarar Jam'iyyar Labour A Legas

  • An raunta mutum daya yayin da wasu da ake zargin yan daba ne suka kai wa tawagar Olumide Oworu hari yayin kamfe
  • Dan takarar majalisar jihar Legas na mazabar Surulere 1, karkashin jam'iyyar Labour ya tabbatar da lamarin a shafinsa na Twita
  • Oworu ya ce sun kai rahoto ofishin hukumar yan sanda na Iponri yana mai cewa Allah ya takaita abin bai wuce hakan ba

Legas - An raunata mutum daya yayin da wasu da ake zargin yan daba ne suka kai hari yayin ralli ta Olumide Oworu, dan takarar majalisar jiha na karamar hukumar Surulere 1 karkashin jam'iyyar Labour.

A wani rubutu da ya yi a shafinsa na Tuwita a ranar Alhamis, Oworu ya ce an kai wa shi da tawagarsa hari a Iponri a Surulere yayin da suke kamfe, The Cable ta rahoto.

Olumide
Yan Daba Sun Kai Hari Yayin Kamfe Din Dan Takarar Majalisa Na Jam'iyyar Labour A Legas. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

Ya ce lamarin ya faru a ranar Talata kuma sun kai rahoto ofishin yan sanda na Iponri.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ga abin da ya rubuta a Twita:

"An kai wa ni da tawaga ta hari a ranar Talata a yayin da muke kokarin yin kamfe a Iponri, Surulere. An raunata mutum daya cikin tawaga ta, amma mun gode Allah abin bai wuce haka ba. An kai kara ofishin yan sanda na Iponri."

Oworu ya yi fice saboda fitowa da ya yi a matsayin 'Tari' a fim mai dogon zango na 'The Johnsons' a Africa Magic.

Ya sanar da sha'awar yin takara na wakiltar Surulere 1 karkashin jam'iyyar Labour a ranar 23 ga watan Fabrairu.

Sanarwar nasa na zuwa watanni kadan bayan cikar wa'adin mika fom din takara ga yan siyasa masu son takarar majalisa - na 8 ga watan Agustan 2022.

Oworu zai fafata wurin neman kujerar wakiltar Surulere 1 da Desmond Elliot, wani jarumin da shima ya zama dan siyasa karkashin jam'iyyar APC.

Mahara dauke da makamai sun kai hari wurin kamfen din Atiku a Kaduna

A baya kun ji cewa wasu mahara da ake zargin yan daban siyasa ne sun kai hari wurin taron yakin neman zaben Alhaji Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, a Kaduna.

Tsohon mataimakin shugaban kasa, ya tabbatar da afkuwar lamarin cikin wani wallafa da ya yi a sahihin shafinsa na Facebook.

Asali: Legit.ng

Online view pixel