Mota Dauke Da Yara Yan Makarantar Firamari Ta Yi Kundunbala A Legas

Mota Dauke Da Yara Yan Makarantar Firamari Ta Yi Kundunbala A Legas

  • Wata motar kai daliban firamari makaranta ta yi hadari a unguwar Surulere a Legas
  • Wani shaidan gani da ido ya ce direban da sauran yara da mai kula da su duk sun jikkata
  • Mutane sun garzaya da daliban da mai kula da su zuwa asibiti yayin da direban ya tsere

Jihar Legas - Wata bas dauke da yara yan makaranta da shekarunsu ya kama daga daya zuwa biyar, a ranar Alhamis, a Legas ta yi kundun bala inda mutum uku suka jikkata.

Lamarin ya faru ne da safe a unguwar Surulere kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Motar kai yara makaranta
Motar kai yara makaranta ta yi hadari a Legas. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yadda hadarin ya faru

Wakilin kamfanin dillancin labarai na kasa, NAN, wanda ya shaida faruwar abin ya ce bas din mai lamba KTU-465DN ta bugi shingen tsakiyar hanya ta banbare simintin da ke rike da fitilar titi, kafin daga bisani ta yi kundunbala.

Kara karanta wannan

2023: Dan Takarar Majalisa da Aka Sace Ya Gudo, Ya Faɗi Abubuwan da Ya Gani a Sansanin 'Yan Bindiga

Mutane da abin ya faru a gabansu sun garzaya wurin suka kuma dauki yaran da mai kula da su a motar, suka garzaya da su asibitin Topaz da ke kusa.

Direban motan, wanda shima ya jikkata, ya tsere daga wurin, ta yi wu saboda tsoron hari daga fusatattun mutane.

A asibitin na Topaz, likitoci da sauran ma'aikatan lafiya sun duba su.

Dakta Sanusi Olatunbosun, wanda ke bakin aiki, daga bisani ya fada wa NAN cewa:

"Mutane bakwai ke cikin bas din yan makarantan, uku sun yi munanan rauni yayin da hudu sun samu kananan rauni."

Olatunbosun ya ce an yi wa dukkan wadanda abin ya faru da su magani kuma an ajiye su na awa biyu a asibitin ana lura da su kafin aka sallame su.

Ya ce asibitin na fatan makarantar za ta biya kudin maganin da aka musu.

Kalamansa:

"Dukkansu idon su biyu kuma an sallame su cikin yanayi mai kyau."

Kara karanta wannan

"Na Taki Sa'ar NYSC": Budurwa Mafi Gajarta Za Ta Auri Dan Bautar Kasa Mafi Tsawo A Sansaninsu, Hotunansu Sun Yadu

Likita ya bukaci iyayen yara su saka ido a kansu

Olatunbosun ya ce ya shawarci makarantar ta fada wa iyayen yaran su rika sa ido sosai a kansu, sannan su bada rahoto idan yaran na samun alamomi kamar jiri, kasala da yawan barci.

Wasu matasa a wurin da hadarin ya faru sun matsar da motar zuwa gefen titi don kare cinkoson ababen hawa.

Jami'an hukumar bada agajin gaggawa na jihar Legas su ma sun isa wurin da abin ya faru don kula da zirga-zirgan ababen hawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel