Yadda Jiga-Jigan PDP a Imo Suka Cinye Kuɗin Zaɓen Atiku, Sakatare

Yadda Jiga-Jigan PDP a Imo Suka Cinye Kuɗin Zaɓen Atiku, Sakatare

  • Sakataren jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na ƙasa, ya zargi wasu jiga-jigan jam'iyyar da yi mata zagon ƙasa
  • Samuel Anyanwu ya bayyana cewa wasu ƙusoshin jam'iyyar sun haɗa baki da APC domin ganin ya faɗi zaɓe a jihar
  • Sakataren jam'iyyar ya sha alwashin nan bada jimawa ba, za a bayyana sunayen baragurbin da suka janyowa PDP matsala a jihar

Jihar Imo- Sakataren jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na ƙasa, Samuel Anyanwu, ya zargi wasu jiga-jigan jam'iyyar a jihar Imo da yiwa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar, Atiku Abubakar, zagon ƙasa a zaɓen shugaban ƙasa.

Anyanwu, ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da kakakin sa, Ikenna Onuoha, ya fitar, inda yayi zargin cewa jiga-jigan jam'iyyar, sun karɓi kuɗin zaɓen da PDP ta bayar sannan suka koma suka yiwa APC aiki. Rahoton Punch

Kara karanta wannan

2023: Ana Dab Da Zaɓe, Jam'iyyar NNPP Ta Watsawa Ɗan Takarar Gwamnanta Baya, Ta Koma Bayan APC

Anyanwu
Yadda Jiga-Jigan PDP a Imo Suka Cinye Kuɗin Kamfen Na Atiku, Sakataren PDP Na Ƙasa Hoto: Daily Post Nigeria
Asali: UGC

Sakataren PDP ɗin ya nuna damuwar sa kan yawan baragurbin dake cikin jam'iyyar a jihar Imo, inda ya ƙara da cewa burin su kawai shine su ga jam'iyyar ta watse a jihar.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Anyanwu ya bayyana cewa babban burin waɗannan baragurbin a zaɓen shugaban ƙasan da ya gabata shine su ga cewa sun hana jam'iyyar da mambobin ta kuɗin da aka ware aka sako saboda zaɓe.
“Ya koka kan yadda suka yi kunnen uwar shegu da kiraye-kiraye da roƙon da akai tayi musu domin su ba waɗanda ya dace kuɗaɗen kamar yadda aka tsara."
"Yayi nuni da cewa dalilin su na yin wannan zagon ƙasan ga jam'iyyar shine domin hana jam'iyyar katabus ta hanyar tabbatar da ƴan takarar ta sun sha kashi a zaɓen."

Kara karanta wannan

2023: Cikin Gwamnan PDP Mai Neman Tazarce Ya Kaɗa, Babbar Jam'iyyar Adawa Ta Koma Bayan Ɗan Takarar APC

“A cewar sa, bayan sun laƙume kuɗin zaɓen, sai wasu daga cikin baragurbin suka juyawa ƴan takarar PDP baya sannan suka koma yiwa jam'iyyar zagon ƙasa domin cika alƙawarin da suka yi da shugabannin jam'iyyar APC.

Sakataren jam'iyyar ya kuma tabbatar da cewa nan bada daɗewa ba za a bayyana sunayen waɗanda suka ci amanar PDP, kowa ya sani. Rahoton Headtopics

Dalilin da Yasa Peter Obi Ya Lashe Kudu Maso Kudu da Kudu Maso Gabas, Okowa

A wani labarin na daban kuma, abokin takarar Atiki ya bayyana dalilin samun nasarar Peter Obi a yankunan Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu.

Peter Obi ya lashe waɗannan yankunan da ƙuri'u masu rinjaye..

Asali: Legit.ng

Online view pixel