Dalilin da Yasa Peter Obi Ya Lashe Kudu Maso Kudu da Kudu Maso Gabas, Okowa

Dalilin da Yasa Peter Obi Ya Lashe Kudu Maso Kudu da Kudu Maso Gabas, Okowa

  • Abokin takarar Atiku Abubakar ya bayyana muhimman abubuwan da suka baiwa Peter Obi nasara a shiyyoyi biyu
  • Gwamna Okowa ya ce fafutukar neman mulki ya koma kudu da Addini na cikin abubuwan da suka taimakawa LP
  • Ya ce mutane sun ba da haɗin kai sun fito zabe amma INEC ta ƙi yin biyayya ga kundin dokokin zaɓe

Delta - Ɗan takarar mataimakin shugaban kasa na PDP, Ifeanyi Okowa, ya ce Peter Obi ya yi amfani da dabaru daban-daban wajen samun nasara a kudu maso kudu da kudu maso gabas a zaben 25 ga watan Fabrairu.

Okowa, gwamna a jihar Delta, ya yi wannan furucin ne a Asaba ranar Litinin yayin da yake tsokaci kan sakamkon zaben shugaban kasa da aka kammala.

Gwamna Okowa.
Dalilin da Yasa Peter Obi Ya Lashe Kudu Maso Kudu da Kudu Maso Gabas, Okowa Hoto: Ifeanyi Okowa
Asali: Twitter

Punch ta rahoto gwamna Okowa na cewa:

Kara karanta wannan

2023: Shugaban APC Na Kasa Ya Fasa Kwai, Ya Ce Zaben Shugaban Kasa Yana da Naƙasu

"Abubuwa da dama sun taka rawa wajen baiwa Obi nasara a shiyyoyin kudu maso kudu da kuma kudu maso gabas. Fafutukar mulkin Najeriya ya koma kudu, Addini da baiwa Inyamurai dama su ne a matakin farko."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Tafiyar Obidient wata tafiya ce da ta mamaye kudu maso kudu da kudu maso gabas, mutane suna ƙaunar Obi domin kawo sauyi, sun yi imani cewa lokacin ya yi da Ibo zai mulki ƙasa."
"Na aminta da cewa mutane sun fito sun sauke hakkinsu amma hukumar INEC ba ta bi kundin dokokin zaɓe ba."

Dangane da batun ko gaskiya ne ya zanta da tsohon gwamna James Ibori, kan makomar PDP a Delta, gwamna Okowa ya ce:

"Wannan sirri ne irin namu na 'yan siyasa, ba zan faɗa maku abinda muka tattauna ba."

Gwamna Okowa ya bayyana cewa yana nan kyam a bayan ɗan takarar gwamna a inuwar PDP, Sheriff Oborevwori, wanda ya samu nasara a zaben fidda gwani.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Lauyoyin Peter Obi sun shiga ganawa da INEC kan wani batu na zaben bana

Bugu da ƙari, Okowa ya ce ya cika dukkan alƙawurran da ya ɗaukar wa mutanen Delta a shekarar 2015, kamar yadda Sahara Reporters ta rahoto.

Shugaban APC Na Kasa Ya Amince An Samu Aibu a Zaben da Tinubu Ya Yi Nasara

A wani labarin kuma Shugaban APC Na Kasa Ya Fasa Kwai, Ya Ce Zaben Shugaban Kasa Yana da Naƙasu

Sanata Abdullahi Adamu ya ce babu inda aka tabba kammala zabe ba tare da samun wata matsala ba, almuhim dai sun cika alkawarin shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel