Zaben Gwamnan Ogun: Jam’iyyu 10 Sun Yi Maja Da PDP Don Daddake Abiodun Daga Kujerar Gwamna

Zaben Gwamnan Ogun: Jam’iyyu 10 Sun Yi Maja Da PDP Don Daddake Abiodun Daga Kujerar Gwamna

  • Tana shirin kwabewa Gwamna Dapo Abiodun na Jihar Ogun yayin da jam’iyyar PDP a jihar ta ce kimanin jam’iyyun siyasa 10 suna aiki don tsige shi daga kujerarsa
  • Gwamna Abiodun, dan takarar APC a zaben gwamnan Ogun na ranar 18 ga watan Maris na neman zarcewa kan kujerarsa
  • Sikiru Ogundele, shugaban PDP a jihar ya bayyana cewa jam’iyyu 10 da wasu fusatattun mambobin APC na aiki tare da babbar jam’iyyar adawar

Ogun - Dapo Abiodun, gwamnan jihar Ogun, na cikin halin fargaba yayin da shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar, Sikiru Olawale Ogundele, ya bayyana cewa jam'iyyun siyasa 10 sun yi maja da jam'iyyar adawar.

Ogundele ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da BBC Yoruba a ranar Asabar, 11 ga watan Maris, mako guda kafin zaben gwamnan da aka daga.

Kara karanta wannan

Hankalin PDP Ya Tashi, APC Ta Samu Gagarumin Goyon Bayan da Zai Ba Ta Nasara a Zabe Na Gaba

Yan takarar gwamna a jihar Ogun
Zaben Gwamnan Ogun: Jam’iyyu 10 Sun Yi Maja Da PDP Don Daddake Abiodun Daga Kujerar Hoto: Dapo Abiodun, Ladi Adebutu
Asali: Twitter

Yadda PDP ta shirya lallasa APC, Dapo Abiodun a jihar Ogun

A cewar shugaban na PDP, wasu fusatattun mambobin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na yi wa babbar jam'iyyar adawa aiki gabannin zaben.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abiodun, dan takarar APC a zaben ranar Asabar kuma gwamna mai ci na neman zarcewa a karo na biyu.

Babban abokin hamayyarsa shine Oladipupo Adebutu, dan takarar gwamna a PDP kuma dan shahararren dan kasuwa Kensington Adebutu, wanda aka fi sani da Baba Ijebu.

INEC ta yaudari yan Najeriya, Inji shugaban PDP reshen Ogun

Shugaban na PDP a jihar ya kuma magantu game da zaben shugaban kasa da na yan majalisar tarayya na ranar 25 ga watan Fabrairu da aka kammala a fadin kasar.

Ya ga laifin hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) da bata bi tsari ba, yana mai cewa zaben shine mafi muni da aka taba yi a tarihin Najeriya.

Kara karanta wannan

Dalilin Da Yasa Ƙawancen Da PDP Ta Yi Da Wasu Jam'iyyu 9 A Kaduna Baya Ɗaga Min Hankali, Uba Sani

A cewar Ogundele, INEC ta yi wa yan Najeriya karya kasancewar ta gaza cika alkawarin da ta yi wa yan Najeriya kan amfani da na'urorin BVAS a ranar zabe.

Kalli bidiyon a kasa:

2024: Dogara na bayan dan takarar APC a zaben gwamnan Bauchi

A wani labarin kuma, tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, ya ayyana goyon bayansa ga dan takarar jam'iyyar APC, Ambasada Abubakar Saddique a zaben gwamnan jihar Bauchi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel