Dalilin Da Yasa Ƙawancen Da PDP Ta Yi Da Wasu Jam'iyyu 9 A Kaduna Baya Ɗaga Min Hankali, Uba Sani

Dalilin Da Yasa Ƙawancen Da PDP Ta Yi Da Wasu Jam'iyyu 9 A Kaduna Baya Ɗaga Min Hankali, Uba Sani

  • Dan takarar gwamna na jihar Kaduna, Uba Sani, ya sanar da cewa bai damu da kawancen da jam'iyyar PDP ta yi da wasu jam'iyyun siyasa 9 a jihar ba
  • Sani ya ce jam'iyyun ba a san su ba, kuma mutanen Jihar Kaduna za su zabe sabon gwamna ne bisa ayyukan da ya yi a baya
  • A cewar Sani, Isah Ashiru, dan takarar gwamna na PDP, ya shafe shekaru 8 a majalisar tarayya amma bai taba gabatar da kudirin doka ko daya ba

Sanata mai wakiltar Kaduna Central kuma dan takarar gwamna na jam'iyyar APC a jihar, Uba Sani, ya ce bai damu da goyon bayan da wasu jam'iyyu ke yi wa babban abokin hamayyarsa, Isa Ashiru Kudan na jam'iyyar PDP ba.

Sani ya bayyana hakan ne cikin wata hira da aka yi da a Arise TV dangane da yiwuwar nasararsa a zaben da ke tafe a jihar.

Kara karanta wannan

Zaben Gwamnan Ogun: Jam’iyyun Siyasa 10 Da Mambobin APC Sun Yi Maja Da PDP Don Tsige Gwamnan APC Daga Mulki

Ashiru da Sani
Uba Sani ya yi martani yayin da wasu yan jam'iyyu tara suka goyi bayan dan takarar PDP. Hoto: Uba Sani.
Asali: Twitter

A kalla yan takarar gwamna na jam'iyyu tara ne a baya-bayan nan suka mara wa Ashiru baya gabanin zaben gwamna.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yan takarar, a karkashin inuwar “The Kaduna State Rescue and Rebuild Gubernatorial Candidates Forum,” sun ce tikitin musulmi da musulmi da APC ta yi dabara ce ta raba kan jihar saboda addini.

Jam'iyyun tara sune , Action Alliance, Young Progressives Party, Allied People’s Movement, Action People’s Party, All Progressive Grand Alliance, da National Rescue Movement, tare da shugabannin Accord Party, Action Democratic Party, da Zenith Labour Party.

Martanin Sanata Uba Sani na jam'iyyar APC mai mulki a Kaduna

A yayin da ya ke tsokaci kan batun, Sanata Uba Sani ya ce jam'iyyun ba su da wani farin jini a jihar da zai isa su daga masa hankali.

Kara karanta wannan

Bago VS Kantigi: Muhimman Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Manyan Yan Takara 2 a Jihar Neja

Ya ce:

"Bari in fayyace maka cewa ban damu da wadannan jam'iyyun da aka ce sun mara wa abokin hamayya na baya makon da ta gabata ba. Mutanen Kaduna suna da wayau. Muna da wayewa, muna da hikimi. Kuma sun san abin da ke faruwa a Jihar Kaduna a siyasance.
"Mutanen Jihar Kaduna za su fita su yi zabe bisa la'akari da ayyukan da aka san kowanne dan takara ya yi. Isah Ashiru, kamar ni, ya wakilci mazabarsa a majalisar tarayya.
"Ya shafe shekara takwas a majalisar tarayya kuma mutanen jihar Kaduna sun sani cewa bai gabatar da ko kudiri guda ba. Don haka sun san wanene shi. Sun san bai cancani zama gwamnan Jihar Kaduna ba.
"Shi yasa ban damu ba. Ban yi mamaki cewa ya fita ya nemi goyon bayan wasu jam'iyyun da ma su da adireshi a jihar Kaduna ba. Shi yasa ban damu ba. Mafi yawancinsu jam'iyyu ne da kawai a takardar zabe suke."

Kara karanta wannan

Shekarau: Dalilin Da Ya Sa Na Shiga Motar Gwamna Ganduje

Martanin Jigon PDP a Kaduna kan kalaman Sanata Uba Sani

Legit.ng ta tuntubi, Sani Sidi Baba jigo a jam'iyyar PDP a Kaduna kuma jami'in tattara sakamakon zabe na babban jam'iyyar hamayar don ji martaninsa kan kalaman Uba Sani.

A cewarsa mutanen jihar Kaduna tabbas sun ga abin da Uba Sani ya yi a majalisa na kawo dokar sauya takardun naira wacce ta jefa talakawa cikin kuncin rayuwa da wahahalu duba da cewa kowa ya san ba mu kai matsayin yin hakan ba a kasar.

Sidi Baba ya ce duk da babban bankin kasa CBN ce ta aiwatar da tsarin amma Uba Sani ya gabatar da kudirin a gaban majalisa har ta zama doka.

Game da zargin cewa Isah Ashiru bai gabatar da kudiri ba, Sani ya ce hakan ba gaskiya bane yana mai cewa:

"Duk abin da ake bukata dan majalisa ya yi na kawo kudirin cigaba a mazabarsa ya yi kuma mutanen mazabarsa sunyi sam barka.

Kara karanta wannan

A Karshe Wike Ya Bayyana Wanda Ya Kori Peter Obi Daga PDP A Yayin Da Rikicin Jam'iyyar Ke Kara Ruruwa

"Misali, makarantun firamari, gyaran cibiyar lafiya, titi, lantarki na hasken rana (solar) da sauransu."

Sidi Baba ya cigaba da cewa:

"Ko zaben yan majalisun tarayya da aka yi a baya za ka ga alamu cewa jam'iyyar mu ta PDP ta fi samun kujerun hakan na nufin mutane sun juya musu baya kuma ko a wannan zaben na gwamna mu za su zaba."

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel