Kotu Ta Amince Wa INEC Ta Gyara Na'urar BVAS, Ta Yi Watsi da Bukatar Obi

Kotu Ta Amince Wa INEC Ta Gyara Na'urar BVAS, Ta Yi Watsi da Bukatar Obi

  • Kotu ta amince wa hukumar INEC ta sake sabunta bayanan na'urar BVAS domin gudanar da zaben 11 ga watan Maris
  • A ranar Laraba, kwamitin alkalai uku na Kotun daukaka kara mai zama Abuja ya yanke wannan hukuncin
  • Peter Obi na Labour Party ne ya bukaci Kotu ta hana INEC aiwatar da haka saboda za'a goge bayanan da ke cikin na'urorin

Abuja - Kotun daukaka ƙara ta sahalewa hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta sake saita na'urar tantance masu kaɗa kuri'a (BVAS) da aka yi amfani da su a zaben shugaban ƙasa.

Kwamitin Alƙalai uku bisa jagorancin mai shari'a Joseph Ikyegh, ya ce sake saita na'aurar zai ba hukumar damar gudanar da zaben gwamnoni da 'yan majalisar jiha ranar 11 ga watan Maris.

Na'urar BVAS.
Malamin zabe na aiki da BVAS Hoto: INECNigeria
Asali: Twitter

Alƙalan sun yanke wannan hukunci ne kan bukatar ɗan takarar shugaban ƙasa na LP, Peter Obi, wanda ya nemi a ba shi dama ya duba kayayyakin da INEC ta yi amfani da su ranar zaɓe.

Kara karanta wannan

Bayan Ya Garzaya Kotu, Peter Obi Ya Aikewa Magoya Bayansa Da Wani Muhimmin Gargaɗi

Daily Trust ta rahoto cewa Kotun ta ƙi amince wa rokon Peter Obi na hana INEC sake kwaskwarima da saita na'aurar BVAS.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kwamitin Alkalan kotun ya amince da buƙatar INEC ne bayan hukumar ta tabbatar da cewa zata sauke dukkan bayanan aikin da na'uroron BVAS 176,000 suka yi a tushen ma'ajiya.

Haka zalika Peter Obi bai kalubalanci wannan ikirararin na INEC ba, bisa haka Alkalan Kotun suka sahalewa bukatar INEC na sabunfa bayanan BVAS don tunkarar zaɓe na gaba.

Bugu da ƙari, Kotun ta amince da bukatar shugaban kasa mai jiran gado, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, na APC, wanda ya nemi a ba shi dama ya duba kayan da aka gudanar da zaɓe da su.

Kotun ta baiwa Tinubu cikakkiyar damar zuwa ya duba kayayyakin da INEC ta yi amfani da su yayin zaben shugaban kasa ranar 25 ga watan Fabrairu, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Muna Jiran Hukuncin Kotun ƙoli Akan Lamarin Shekarau Inji NNPP

Kotun koli ta raba gardama kan tikitin APC a Akwa Ibom

A wani labarin kuma Kotun Koli Ta Tabbatar da Nasarar Ɗan Takarar Gwamnan APC a Akwa Ibom

Kwamitin alkalan Kotun ya bayyana cewa Mista Udofia ne halastaccen ɗan takarar gwamnan Akwa Ibom a inuwar APC.

Tsohon Sanata ne ya nemi Kotun ta kwace takara ta miƙa masa saboda wasu dalilai da ya zayyana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel