'Yan Boko Haram Sama da 1000 Sun Mika Wuya Bayan ISWAP Ta Kashe 200

'Yan Boko Haram Sama da 1000 Sun Mika Wuya Bayan ISWAP Ta Kashe 200

  • Mambobin kungiyar Boko Haram sama da 1000 tare da iyalansu sun mika wuya ga rundunar soji
  • Bayanai sun nuna cewa an sami wannan ci gaba ne bayan ISWAP ta matsa musu lamba da kisa
  • Wata majiyar sojoji ta ce yan ta'addan da suka miƙa wuya sun ce sun rasa maɓoya ne saboda fargaba

Borno - Aƙalla mayakan kungiyar ta'addanci Boko Haram 1,250 ne suƙa miƙa wuya ga sojojin Najeriya tare da iyalansu a arewa maso gabas cikin kwanaki 7 da suka shige.

Rahoto ya nuna cewa hakan ba zai rasa alaƙa da artabun da suka yi da ƙungiyar ISWAP da basu ga maciji, lamarin da ya yi ajalin mayaƙan Boko Haram sama da 200.

Mayakan Boko Haram da iyalansu
Yan ta'addan Boko Haram da suka mika wuya tare da iyalansu Hoto: ZagazolaMakama
Asali: Twitter

Masani kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, Zagazola Magama, ya tattaro yadda ISWAP ta kai harin ɗaukar fansa kan mayaƙan Boko Haram ranar 26 da 27 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Yan Ta'addan ISWAP Sun Hallaka Yan Boko Haram Sama Da 200 a Borno

Ya ce lamarin ya faru ne a garuruwan Gaizuwa, Mantari, Gabchari, Kashimiri da Maimusari, karamar hukumar Bama da ke arewa maso gabashin jihar Borno.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mayakan ISWAP sun samu nasarar fatattakar Boko Haram, suka sheƙe da yawa daga cikinsu kana suka tilastawa sauran ƙaura daga matsugunansu tare da iyalansu.

Wata majiya daga rundunar sojin Najeriya ta tabbatarwa Zagazola Makama cewa ISWAP ta tare yan Boko Haram a Yale, Konduga da Choliye da ke Gudunbali, inda suka kashe akalla 200.

Meyasa suka miƙa wuya ga Sojoji?

Majiyar ta ce:

"Yan ta'addan sun miƙa wuya ne saboda fargabar rasa rayuwarsu hannun Jirgin yakin Super Tucano ko ISWAP, ba su da wurin guduwa. Zuwa yanzun mayaka 1,250 tare da iyalansu sun miƙa wuya a cikin mako ɗaya."
"Wannan shi ne adadi mafi yawa da suka miƙa wuya cikin kankanin lokaci kuma sun miƙa wuya tare da dabbobin kiyo kusan 1000. Sun ce mayakan ISWAP na farautar rayukansu kuma ba su barin mata ko yara, kashe kowa su ke."

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kutsa Har Ciki Fada, Sun Yi Garkuwa da Matan Sarki 2 da Ɗansa a Jihar Arewa

"Daga cikinsu har da mata, waɗanda yan ta'addan suka maida bayi da kuma ƙananan yaran da suka haifa wa yan ta'addan."

A cewar majiyar, suna ci gaba da tattara bayanan waɗanda suka tuba kafin daga bisani su miƙa su hannun hukumomin da ya dace domin ɗaukar mataki na gaba.

Wannan yawan miƙa wuyar na da alaƙa da mutuwar shugaban Boko Haram, Abubkar Shekau, wanda ya tashi kansa daga aiki a watan Mayu, 2021 lokacin artabu da ISWAP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel