Da Zafi Zafi: Jam'iyyun PDP, LP, ADC Sun Buƙaci Shugaban INEC yayi Murabus Tare Da Sake Sabon Zaɓe

Da Zafi Zafi: Jam'iyyun PDP, LP, ADC Sun Buƙaci Shugaban INEC yayi Murabus Tare Da Sake Sabon Zaɓe

  • Jam'iyyar PDP, ADC Da Labour Party sun haɗa Kai domin Ganin An sake Zaben Shugaban Ƙasa na Ranar Asabar.
  • Ɗaya Daga Cikin Dalilin da Suka Bayyana Shine, INEC Taƙi Ta Ɗaura Sakamakon Zaɓen a Kundin Tattara Bayanai na Yanar Gizo Gizo
  • Sun Cire Rai Za'ai Musu adalci inda Suka Zargi Sakin Sakamakon Zaɓen ta Hanyar Rubutu, Ya Taɓa Muhibbar Zaɓen Gabaki Ɗaya.

Abuja - Ana cigaba da samun halin ɗarɗar ga jam'iyyu da suke ganin yanayin sakamakon zaɓen da aka gudanar na ranar asabar din data gabata ba bai musu kyau ba.

Biyo bayan balahirar da ake ta samu ne haɗakar jam'iyyun siyasa na PDP, LP da ADC suka miƙa wasu buƙatu ga Hukumar Zaɓe ta Kasa INEC.

Buƙatun da jam'iyyun suke fatan ganin an tabbatar musu da su shine, na fatan ganin an sake sabon zaɓen shugaban ƙasa fil.

Kara karanta wannan

Zaɓukan 2023: Tinubu ya Aikawa Atiku da Obi Ƙwaƙwƙwaran Saƙo Bayan INEC Ta Ayyana Shi a Matsayin Mai Nasara

Iyorciha
Shugaban PDP yace Shugaban INEC yayi Murabus Tare Da Sake Sabon Zaɓe Hoto: Official PDP
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar su, zaɓen shugaban ƙasar da da aka yi na ranar 25 ga watan Fabrairu an tafka magu-magu da ɗungushe maras misaltuwa.

Shugaban jam'iyyar LP dana PDP Iyorchia Ayu da kuma takwaran su na ADC Ralph Nwosu ne suka gabatar da wata haɗakar sanarwar ujila a cikin wata hira da sukayi da manema labarai a Abuja yau talata.

Jam'iyyun guda uku sun ce, rashin ɗaura sakamakon zaɓen na shugaban ƙasa a kundin tattara bayanai na yanar gizo gizo da hukumar take dashi, abune da bazai amsu ba kuma bazai haifar da ɗa mai ido ba.

Shugabannin sun zargi Hukumar INEC ɗin da canja fasalin sakamakon, musamman ma na ƴan majalisa da kuma shugaban ƙasa da akayi.

Inda sukace abinda ake faɗa bashi akayi a rumfunar zaɓe ba. Wanda hakan shine a ganin su dalili da zaisa ita INEC ɗin taƙi ɗaurawa.

Kara karanta wannan

Atiku da Obi suyi koyi da Jonathan su kira Tinubu a waya su tayashi Murna - APC

Ga abinda Abure ya faɗa Channelstv a madadin sauran jam'iyyun:

"Wannan zaɓen ba sahihi bane ko kaɗan"

Ya ƙara da cewa:

"Ana lalata sakamakon zaɓen wuraren da abokan hamayya ke da ƙarfi sosai abune mai ɓata rai".

Saboda haka ne, jam'iyyun yanzu dai kafatanin jam'iyyun basa tunanin za'a iya musu adalci, sannan kuma basu yarda da shugaban INEC Mahmood Yakubu ba kwata - kwata.

Wannan dalili yasa suke kiran sa da kakkausar murya daya sauka nan take. ya bawa mutumin da baida ra'ayi a siyasa yazo ya amshi muƙamin domin a sake sabon zaɓe.

LP, PDP da ADC dai, sun ce ƙin ɗaura sakamakon zaɓen a matattarar bayanai ta INEC ba wani abu bane face saɓawa kundin tsarin mulkin INEC sashi na 60, Doka ta shekarar 2022. Saboda haka bazasu lamun ta ba.

Tuni dai jam'iyyun guda uku suka ce, INEC ta gama nuna musu "Banbanci na ƙwara-ƙwatan" akan abinda wakilan jam'iyyun suka gabatar da kuma abinda ita INEC ɗin take bayyanawa Abuja basa zuwa daidai.

Kara karanta wannan

Zaɓen 2023: Wasu Abubuwa 5 Da Suka Taimaka Wajen Samun Rashin Nasarar Rabiu Kwankwaso

A ƙarshe suka ce, sakin sakamakon zaɓen ta hanyar rubutu, ya taɓa muhibbar zaɓen gabaki ɗaya.

Lalong Ya Tunkuyi Ƙasa a Takarar da Yayi Ta Sanata

Gwamna Lalong yasha kayi ne a hannun ɗan takarar jam'iyyar PDP mai suna Napoleon Bali.

Jaridar Legit Hausa ta ambato cewa Lalong yayi takara a cikin inuwar jam'iyyar APC kuma ya samu ƙuria guda 91, 674, yayin da Bali wanda yayi nasara ya samu ƙuri'u 148,844.

Asali: Legit.ng

Online view pixel