Atiku da Peter Obi Sun Ki Sallamawa Bola Tinubu, Sun Fadi Matsayar da Za Su Dauka
- Atiku Abubakar da ya yi takarar shugabancin kasa a jam’iyyar PDP bai yarda da zaben 2023
- Shi ma Peter Obi na LP ya kalubalanci sakamakon zaben da aka fitar, ya nuna za su shiga kotu
- Jam’iyyar NNPP da ta ba Rabiu Kwankwaso takara ta na ganin INEC ba tayi zaben kwarai ba
Abuja - ‘Dan takaran PDP a zaben shugaban kasa, Atiku Abubakar da Peter Obi na jam’iyyar LP sun ce za su shigar da kara a kotu a kan zaben 2023.
‘Yan takaran sun bayyana haka ne bayan da aka ayyana Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zabe. Daily Trust ta fitar da rahoton a ranar Alhamis.
Dino Melaye wanda shi ne Daretan hulda da jama’a na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa a PDP ya fitar da wani jawabi a yammacin Laraba.
Sanata Dino Melaye ya ce babu ja da baya a yunkurinsu na ganin sun karbe nasarar da suka samu a zabe, jigon na PDP yana ganin an yi magudin zabe.
Ba za ta sabu ba - Dino
"Kira ga daukacin magoya bayan Atiku Abubakar a duk fadin Duniya da cewa ka da ku damu. Ko da an yi kuka yanzu, murna ta na tafe daga baya.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Mummunar rashin adalcin nan ba zai tafi a haka ba. Babu ja da baya a wajen gwagwarmayarmu na karbo nasararmu da aka sace. Za mu samu nasara."
- Dino Melaye
A rahoton dai, an ji Sanata Yusuf Datti Baba-Ahmed wanda ya shiga takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar LP yana cewa za su nemi hakkinsu a kotu.
Yusuf Datti Baba-Ahmed ya yi magana
Yusuf Datti Baba-Ahmed ya ce za su kalubalanci nasarar APC a zaben ne ta hanyar lalama.
Da ya kira wani taron ‘yan jarida a madadin Peter Obi a ranar Laraba, tsohon Sanatan ya tabbatarwa magoya bayansu cewa ba su yarda da zaben nan ba.
A cewar Datti Baba-Ahmed zaben da aka yi bai cika sharudan gaskiya da adalci ba, amma duk da haka ya godewa dinbin mutanen da suka zabi jam’iyyarsu.
Farfesa Rufai Alkali a matsayinsa na shugaban NNPP na kasa ya soki hukumar INEC, yake cewa zaben bai yi kyau ba, ya bukaci a shirya wani sabon zabe.
Abubuwan ban mamaki 11
A jerin abubuwan ban al'ajabi a zaben 2023, mun kawo batun Peter Obi da ya samu kuri’u 582,454 a Legas, ya jijjiga Bola Tinubu da ya samu kuri'u 572, 606.
Sannan ‘Dan takaran PDP, Atiku Abubakar ya rasa jihar Delta duk da ya dauko Gwamna Ifeanyi Okowa, NNPP kuwa ta takawa kowa burki a jihar Kano.
Asali: Legit.ng