Jerin Gwamnonin Da Suka Lashe Kujerun Sanatoci a Jihar Su

Jerin Gwamnonin Da Suka Lashe Kujerun Sanatoci a Jihar Su

  • Gwamnoni da dama sun nemi takarar kujerar sanatoci a jihohin su domin zuwa majalisar dattawan Najeriya
  • Sai dai wasu daga cikin gwamnonin jikin su ya gaya musu domin ba suyi nasara ba a takarar da suka yi
  • Ƴan kaɗan ne kawai daga cikin gwamnonin da suka yi takarar kujerun sanatoci suka samu nasara a zaɓen

Wani lamari mai matuƙar ban mamaki shine yadda wasu gwamnonin da suka so su wakilci mutanen su a majalisar dattawa, suka sha kashi a hannun ƴan takarar jam'iyyun adawa.

Wannan zaɓen da aka kammala na shugaban ƙasaa da na ƴan majalisun tarayya a ranar Asabar, ya nuna gazawar wasu gwamnoni a yankunan su, da kuma yadda mutane suka tsaya suka kare abinda suke ra'ayi.

Yayin da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ke cigaba da tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasa, ƴan takarar da suka neman kujerun sanatoci tuni suka san matsayar su.

Kara karanta wannan

Sakamakon Zabe: Tsoffin Gwamnoni da Ministoci, Sanatoci da Wasu Manya Sun Huro Wa INEC Wuta Kan Abu 1

Bello da Umahi
Jerin Gwamnonin Da Suka Lashe Kujerun Sanatoci a Jihohin Su Hoto: Facebook/Governor Of Niger State/Dave Umahi Nweze
Asali: UGC

Gwamnoni biyu sun yi nasara

Sai dai daga cikin gwamnonin da suka yi takarar sanata a jihohin su, guda biyu ne kawai suka samu nasara.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ga jerin su:

Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi

Gwamna David Umahi ya samu nasarar lashe zaɓen sa domin wakiltar Ebonyi ta Kudu a majalisar dattawa.

Umahi, wanda shine ɗan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ya samu ƙuri'u 28,378, inda ya doke ɗan takarar Labour Party, Linus Okorie, wanda ya samu ƙuri'u 25,496

Gwamna Abubakar Bello na jihar Neja

A ranar Litinin, 27 ga watan Fabrairun 2023, gwamna Abubakar Bello na jihar Neja ya lashe zaɓen sanatan Neja ta Arewa a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Gwamna Bello, ya samun nasara bayan ya samu ƙuri'u masu rinjaye a zaɓen inda ya samu ƙuri'u 100,197, domin kayar da ɗan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Shehu Muhammad Abdullahi, wanda ya samu ƙuri'u 88,153.

Kara karanta wannan

Abin Ban Takaici Cocin Gidan Gwamnati Ta Aso Rock Za'a Rufe ta Na Tsawon Shekara 4 - Okowa

Gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu, yakamata ace ya shigo cikin wannan jerin, sai dai a zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, hukumar INEC ta bayyana zaɓen jihar a matsayin ba kammalalle ba saboda zargin an yi ba daidai ba a cikin sa.

Duniya Rawar Ƴan Mata: Lalong Ya Tunkuyi Ƙasa a Takarar da Yayi Ta Sanata

A wani labarin na daban kuma, gwamnan jihar Plateau yasha kashi a takarar nemsn kujerar sanata.

Gwamnan ya sha kashi ne a hannun ɗan takarar jam'iyyar PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel