Jam'iyyar APC Ta Lashe Kujerun Ƴan Majalisar Tarayya 8 a Jihar Jigawa, Ta Rasa 3

Jam'iyyar APC Ta Lashe Kujerun Ƴan Majalisar Tarayya 8 a Jihar Jigawa, Ta Rasa 3

  • Jam'iyyar APC a jihar Jigawa ta samu nasarar lashe mafiya yawan kujerun ƴan majalisar tarayya a jihar
  • Gudaji Ƙazaure yana daga cikin ƴan majalisun da aka dawo da su gida a zaɓen da aka gudanar ranar Asabar
  • Sai dai jam'iyyar ta APC ta sha kashi a hannun jam'iyyar adawa ta PDP a kujerar sanata

Jihar Jigawa- Jam'iyyar All Progressives Congress (APC), mai mulki a jihar Jigawa lashe kujerun ƴan majalisar tarayya guda takwas daga cikin sha ɗaya da ake da su a jihar.

Sai dai jam'iyyar ta rasa sauran ragowar kujerun guda uku a hannun jam'iyyun adawa.

Jam'iyyar APC ta rasa kujerun ƴan majalisar Birnin Kudu da Buji a hannun jam'iyyar PDP. Rahoton Premium Times

Jam'iyyar APC
Jam'iyyar APC Ta Lashe Kujerun Ƴan Majalisar Tarayya 8 a Jihar Jigawa, Ta Rasa 3 Hoto: The Punch
Asali: Twitter

Haka kuma ɗan takarar jam'iyyar APC a kujerar ɗan majalisar tarayya ta Gwaram, Isah Idris, ya sha kashi a hannun ɗan majalisa mai ci yanzu, Yusuf Galambi, na jam'iyyar New Nigeria People Party (NNPP).

Kara karanta wannan

Zaɓen 2023: Atiku Ya Tumurmusa Tinubu a Bauchi, Ya Bashi Tazara Mai Yawa

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hukumar INEC ta kuma bayyana Dahiru Make na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe kujerar ɗan majalisar tarayya ta Dutse/Kiyawa.

Ya samu ƙuri'u 47,836 inda yayi nasara akan ɗan takarar APC mai ci yanzu, Abdullahi Kyamba, wanda ya samu ƙuri'u 36,718.

A kujerar ɗan majalisar tarayya ta Hadejia, Auyo daKafin-Hausa, Ibrahim Usman, na jam'iyyar APC, ya samu ƙuri'u 56,891, inda yayi nasara akan ɗan takarar jam'iyyar PDP, Suleiman Sidi, wanda ya samu ƙuri'u 40,628.

A mazaɓar Gudaji Kazaure ta Kazaure/Roni/Gwiwa da Yankwashi, ɗan takarar jam'iyyar APC, Muktar Muhammad, ya lashe zaɓen inda ya samu ƙuri'u 49,301, inda yayi nasara a kan Hamza Ahmed na PDP, wanda ya samu ƙuri'u 29,655.

A mazaɓar Kirikasamma/Birniwa da Guri, ɗan takarar jam'iyyar APC, Abubakar Fulata, ya samu nasara da ƙuri'u 44,692, inda ya doke ɗan takarar jam'iyyar PDP, Abba Daguro, wanda ya samu ƙuri'u 30,654.

Kara karanta wannan

Sakamakon Zaɓe: Tinubu da Atiku Sun Sha Kashi Hannun Peter Obi a Nasarawa

Haka kuma jam'iyyar APC ta lashe kujerun ƴan majalisar tarayya a mazaɓun Ringim/Taura, Jahun/ Miga, Babura/Garki da Malammadori/Kaugama na jihar.

Sai dai, jam'iyyar ta rasa wasu kujerar Sanatan Jigawa ta Tsakiya a hannun jam'iyyar PDP. Rahoton The Punch

Atiku Abubakar Ya Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa a Jihar Bauchi

A wani labarin na daban kuma, jam'iyyar APC ta sha kashi a hannun jam'iyyar PDP a jihar Bauchi, a zaɓen shugabam ƙasa.

Ɗan takarar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya lallasa Tinubu a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel