Dan Takarar Gwamnan APC a Jihar Enugu Ya Tsallake Rijiya da Baya

Dan Takarar Gwamnan APC a Jihar Enugu Ya Tsallake Rijiya da Baya

  • Yan bindiga sun bude wa ayarin ɗan takarar gwamnan jihar Enugu na APC wuta ranar Laraba da yamma
  • Wani ganau ya bayyana cewa abu guda ya tseratar da ɗan takarar amma da tuni sai labarinsa ake sun kashe shi
  • Mamban kwamitin kamfe ya ce da taimakon Allah kaɗai suka tsira daga mummunan harin

Enugu - Tsagerun yan bindigan da ba'a sani ba kusan su 15 sun farmaki ayarin Chief Uche Nnaji, ɗan takarar gwamnan jihar Enugu a inuwar jam'iyyar APC ranar Laraba da yamma.

A cewar wani ganau, maharan sun mamayi Nnaji a kauyen Agbani kana suka bude masa wuta yayin da motarsa ke kokarin wucewa, kamar yadda Tribune ta rahoto.

Taswirar jihar Enugu.
Dan Takarar Gwamnan APC a Jihar Enugu Ya Tsallake Rijiya da Baya Hoto: Punchng
Asali: UGC

Ya ce yan ta'addan sun ci gaba da harbi ba kakkautawa da nufin kashe mai neman zama gwamna a inuwar APC a zaben 11 ga watan Maris, 2023.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Kutsa Cikin Gidan, Sun Harbe Shugaban Jam'iyya Har Lahira

Sai dai rahotanni sun bayyana cewa maharan ba su cimma manufarsu ba yayin da jami'an tsaron da suke tare da ɗan takarar suka nuna jajircewa wajen maida musu martani.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yan sandan da ke cikin Ayarin suka fara hanzarin maida martanin wuta, aka yi artabu har suka samu nasarar sheƙe ɗaya daga cikin yan bindigan.

Shaidan gani da ido ya ce ganin ɗaya daga cikinsu ya faɗi ƙasa matacce, nan take maharan suka ja da baya, sannan suka ja abin hawansu suka tsere.

"Yadda kasan ruwan harsasai aka yi wa Motar Jeep ɗin, abun mamakin ko ɗaya bai fasa ya shiga ciki ba. Ina da tabbatacin abu ɗaya da ya sa Nwakaibie ke raye har yanzun shi ne Motar sulƙen da yake ciki."

"Ba don wannan motar ba da bani da tantama sai sun kashe shi," inji mutumin yayin hira ta wayar tarho.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Kaiwa Ayarin Ɗan Takarar PDP Kazamin Hari Ana Jibi Zaɓe

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, mamban kwamitin kamfen ɗan takarar gwamnan, Ephrwim Osondu, ya ce biyu daga cikin Direbobin motocin ayarin sun samu raunuka, suna Asibiti ana masu magani.

"Allah ne ya kawo mana ɗauki muka tsira daga hari jiya, muna cikin tafiya daidai Agbani, ba zato maharan suka bude mana wuta har sai da yan sanda suka maida nartani."
"Garin musayar wuta ne ɗaya daga cikinsu ya faɗi ƙasa, daga nan suka tsere."

'Yan Bindiga Sun Kashe Shugaban Jam'iyar APGA Na Gunduma a Ebonyi

A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Kutsa Cikin Gidan, Sun Harbe Shugaban Jam'iyya Har Lahira

Wasu mahara sun shiga har cikin da tsakar dare, sun harbe shugaban jam'iyar APGA na wata gunduma a jihar Ebonyi.

Rahotanni sun bayyana cewa yana kwance a gida da kusan karfe 11 na daren jiya Laraba, ba zato maharan suka kutsa cikin gidan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel