Yan Bindiga Sun Farmaki Ayarin Dan Takarar PDP a Enugu, Sun Kashe Direba

Yan Bindiga Sun Farmaki Ayarin Dan Takarar PDP a Enugu, Sun Kashe Direba

  • Awanni gabanin zaben ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu, yan bindiga sun kai wa ayarin ɗan takarar PDP hari a Enugu
  • Rahotanni sun nuna cewa harin na zuwa ne jim kaɗan bayan wasu mahara sun kashe ɗan takarar Sanatan Enugu ta gabas
  • Duk da babu wani bayani a hukumance daga hukumar 'yan sanda, an ce maharan sun kashe Direban mota ɗaya

Enugu - Wasu miyagun 'yan bindiga sun kai kazamin hari kan ayarin tawagar kamfen ɗan takarar jam'iyyar PDP na mazaɓar mamban majalisar tarayya mai wakiltar Enugu ta Arewa/Kudu, Oforchukwu Egbo.

Jaridar Punch ta tattaro cewa lamarin ya faru ne a yankin Eke-Otu, Amechi Awkunanaw, ƙaramar hukumar Enugu ta kudu ranar Laraba, 22 ga watan Fabrairu, 2023.

Harin yan bindiga
Yan Bindiga Sun Farmaki Ayarin Dan Takarar PDP a Enugu, Sun Kashe Direba Hoto: punchng.com
Asali: Twitter

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun halaka ɗaya daga cikin Direbobin motocin ayarin ɗan takarar PDP a zaben ranar Asabar mai zuwa.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kashe Ɗan Takarar Sanata da Wasu Mutane 5 Saura Kwana 3 Zaɓe

Haka zalika bayan kashe direban, wasu bayanai sun nuna cewa maharan sun kona gawarsa tare da motar da yake ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit.ng ta rahoto cewa wannan na zuwa ne awanni kaɗan bayan wasu yan ta'adda sun kashe ɗan takarar Sanatan Enugu ta gabas a inuwar Labour Party, Mista Oyibo Chukwu.

Rahoton da jaridar Vanguard ta tattaro ya nuna cewa maharan sun haɗa da magoya bayansa 5 da ke tare da shi a Mota, sun halaka su sannan suka kona motar.

Duk wani yunkuri na jin ta bakin jami'in hulɗa da jama'a na rundunar yan sandan jihar Enugu, DSP Daniel Ndukwe, ya ci tura domin lambar tarhonsa ta ƙi shiga har zuwa yanzu da muke haɗa wannan rahoton.

Ranar Asabar da ke tafe watau nan da awanni 48, 25 ga watan Fabrairu, 2023, hukumar zabe ta ƙasa INEC ta tsara gudanar da zaben shugaban kasa, Sanatoci da yan majalisar wakilai.

Kara karanta wannan

CBN Zai Haramta Tura Kuɗi Ta Asusun Banki a Lokacin Zaben 2023? Gaskiya Ta Bayyana

Yan bindiga sun sace shugabanni 2 a Kaduna

A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Shugaban PDP da Jagoran Al'umma a Kaduna

Mazauna yankin sun bayyana cewa wannan ne karo na farko da 'yan ta'addan suka aikata makamancin haka a kauyen Dan Mahawayi dake Giwa a Kaduna.

A cewarsu, yan bindigan sun saje da tawagar kamfen ɗan takarar majalisar tarayya mai wakiltar Birnin Gwari da Giwa, sannan suka aikata ta'adin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel