Mafarauci Ya Bankado Dubban Katunan Zabe a Dajin Anambra

Mafarauci Ya Bankado Dubban Katunan Zabe a Dajin Anambra

  • Yan kwanaki kafin babban zaben shugaban kasa, wani mafarauci a jihar Anambra ya zakulo katunan zabe masu yawan gaske a wani jeji
  • Rahoto ya nuna cewa mafaraucin ya bankado dubban katunan zabe da aka zuba a wata jaka sannan aka jefa ciki duron a yankin Nnewi
  • Rundunar yan sanda ta yi martani kan lamarin inda ta ce ta shiga bincike don gano gaskiyar lamari

Rahotanni sun kawo cewa wani mafaruci ya tsinci dubban katunan zabe na PVC a wani jeji da ke yankin Nnewi na jihar Anambra.

Amaka Nwafor, wata mai gabatar da shirye-shirye a Authority FM, ta ce wani mafarauci ya tsinci katunan zabe a ranar Talata, a jejin Akamili, karamar hukumar Nnewi ta arewa, rahoton The Cable.

Katunan zabe jibge a kasa
Mafarauci Ya Bankado Dubban Katunan Zabe a Dajin Anambra Hoto: Daily Post
Asali: UGC

Ta ce katunan zaben sun kasance a cikin wasu jakunkuna biyu sannan an jefa su a cikin wata bakar randa, tana mai cewa bayan ya gano su, sai mafaraucin ya kai su harabar gidan radiyon.

Kara karanta wannan

'Cashless': Maroki ya waye, ya buga kalangu a wani bidiyo, ya ba lambar akanta

Nwafor ta ce katunan zaben da aka duba zuwa yanzu mallakin al'ummar yankin karamar hukumar Nnewi ta arewa ne.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Saboda haka, ta yi kira ga wadanda aka ce masu ba a ga PVC dinsu ba da su garzayo gidan radiyon domin duba katunan zabensu.

Martanin rundunar yan sandan Najeriya

A halin da ake ciki, a wata sanarwa da kakakin yan sandan jihar, Tochukwu Ikenga, ya fitar, ya ce rundunar bata samu kowani rahoto mai kama da haka ba, rahoton Punch.

Sanarwar ta ce:

"Dangane da haka, kwamishinan yan sanda, CP Echeng Echenghas, ya yi umurnin bincike kan bidiyon don gano lamuran da ke kewaye da shi da kuma yiwuwar kama wadanda ake zargi kan lamarin."

Duk wanda bai gamsu da sakamakon zabe ba ya tafi kotu, Buhari ga yan takara

A wani labarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga masu neman takarar kujerar shugaban kasa a zaben ranar Asabar da su guji tayar da tarzoma bayan sanar da sakamkon zaben.

Buhari ya bukaci duk dan takarar da bai gamsu da sakamakon zaben ba da ya garzaya kotu domin shari'a ta yi aikinta maimakon rura wutar fitina tsakanin al'ummar kasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel