‘Fidelity’: Maroki Ya Buga Roko, Attajira Ta Nemi Ya Ba da Lambar Asusu, Martaninsa Ya Ba da Nishadi

‘Fidelity’: Maroki Ya Buga Roko, Attajira Ta Nemi Ya Ba da Lambar Asusu, Martaninsa Ya Ba da Nishadi

  • Bidiyon wani maroki ya jawo cece-kuce da nishadi a kafar sada zumunta ganin yadda ya zo da sabon salo
  • Ganin cewa babu tsabar kudi a hannun jama’a a kasar, marokin ya nemi a tura masa kudi asusunsa na banki
  • An ji mutumin na ambatan sunan wani banki daga cikin fitattun bankunan kasar nan, ya fadi lambar akant

Maroki ya kada gurmi ga wata mata a daidai lokacin da Najeriya ke fuskantar karancin tsabar kudi, ya ba da mamaki.

A wani bidiyon da ya yadu a kafar sada zumunta ta Instagram, an ga marokin tare da dan amshinsa suna rera wakar yabo ga wata mata.

Matar da suke kada wa roko na zaune a cikin mota, sai ta tambaye su lambar asusun banki sai kawai ya fara fadi a cikin wakar.

Kara karanta wannan

Karancin Naira: Mutane Sun Banka Wa ATM Wuta Saboda Abu 1 Da Ya Faru Ana Cikin Cire Kuɗi

Maroki ya zo da sabon salon roko
Hotn marokin da ya ba lambar akant a zuba masa kudi | Hoto: @onlyinnigeria
Asali: Instagram

Bayan fadin lambar asusu, sai aka tambaye shi sunan banki, shi kuwa ya amsa da ‘peedility’, ma’ana bankin Fidelity.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kalli bidiyon:

Martanin jama’a

Jama'ar kafar Instagram sun ce ba za a yi babu su ba, sun nishadantu da wannan kidi, sun yi martani mai daukar hankali. Ga kadan daga ciki:

jesichun:

"Ina kaunar kasar nan!!!"

temi_are39:

"Wannan mutumin ya nishadantar dani...bari na tura masa wani abu fiifiliti.”

isimemematt:

"Bari naje na turawa wadannan mutanen wani abu. Ya min dadi.”

radcheval:

"A bar batun a gefe, wannan Yarbanci ne da tsarmin Arewa? Ban san ‘yan Arewa na amfani da ganga irin wannan ba su ma.”

lammylinky:

"....matukar baka karbar tiransfa a wannan yanayin da kasar ke ciki ka yi kuskure.”

yackzofficial:

"Peediliti"

onyeubanatu1:

"Baba ka duba FeeDeeLeeTee dinka.”

Kara karanta wannan

Ka taka wuta: Takalmin karfen da aka kera ya girgiza intanet, jama'a sun yi martani

adamzandevez:

"Kai dole na tura wani abu domin na nishadantu.”

mg_pixels_:

"Zan tura masa kudi yanzu-yanzu.”

janetheconsulgeneral:

"Pidility kalli nishadin ‘cashless’.”

itscampbell.e:

"Wannan ci gaba ne mai kyau. Ni fa na jima bana rike tsabar kudi tun 2020. Mahajojin biyan kudi sun mamaye komai. Naija na bukatar ta girma.”

A halin da ake ciki, 'yan Najeriya na ci gaba da fuskantar tashin hankalin karancin sabbin Naira, hakan na shafar kasuwanci da harkokin yau da kullum a bangarori daban-daban na kasar, musamman yayin da aka kusa zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel