Bani da matsala idan na faɗi zaben shugaban kasa, Kwankwaso

Bani da matsala idan na faɗi zaben shugaban kasa, Kwankwaso

  • Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP yace amincewa da shan kaye a zabe ba sabon abu bane a wurinsa
  • Sanata Rabiu Kwankwaso ya yi jawabi a wurin taron da UNIABUJA ta shirya wa masu neman zama shugaban kasa a 2023
  • Tsohon gwamnan Kanon ya ce zuwan NNPP cikin tseren ya samarwa yan kasa zaɓi baya ga APC da PDP

Abuja - Rabiu Musa Kwankwaso, ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar NNPP ya ce ba shi da wata matsala game da amincewa da rashin nasara a zaɓe.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa Kwankwaso ya bayyana haka ne a wurin taron mahawarar yan takarar shugaban kasa da aka shirya a jami'ar Abuja (UNIABUJA).

Rabiu Kwankwaso.
Bani da matsala idan na faɗi zaben shugaban kasa, Kwankwaso Hoto: @KwankwasoRM
Asali: Twitter

A fagen tambayoyi da amsoshi a wurin taron, wani ɗalibi ya tambayi Kwankwaso cewa ko zai amince da sakamakon zaben shugaban kasa mai zuwa idan bai samu nasara ba?

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Bayan Gazawar APC da PDP, Yan Najeriya Suna da Wani Zabi Ɗaya Rak

Da yake amsa wannan tambaya, tsohon gwamnan jihar Kano ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"A shekara 30 da ta wuce, na nemi takara sau 18, na yi nasara 15, na sha kaye sau uku, karo na farko da na sha ƙasa a zabe shi ne a 2003 lokacin ina kan kujerar gwamna."
"Ina da yakinin ni ne gwamna ko shugaban kasa na farko, wanda ya sha kaye a zabe, ya ɗauki mataimakinsa, kwamishinoni da sauran manyan kusoshin gwamnati muka je taya wanda ya samu nasara murna har gida."
"Saboda haka ban da wata damuwa wajen rungumar kaddarar rashin nasara a zaɓe. Na maimaita haka a Legas 2015 (zaben fidda gwanin APC) Buhari ya zo na ɗaya, na zama na buyu, Atiku na uku da Rochas na hudu."

Tsohon gwamnan ya kara da cewa duk da ya san akwai matsaloli a zaben amma bai gardama ba ya amince da rashin nasara.

Kara karanta wannan

2023: Babban Jigon PDP Ya Faɗi Sunayen Jihohin Da Atiku Zai Sha Kaye a Zabe Da Dalilai

"Duk da haka fatana INEC da sauran masu ruwa da fsaki zasu yi abinda ya dace su shirya sahihi kuma karbabben zabe," inji Kwankwaso.

Jaridar Punch ta tattaro Kwankwaso na cewa shigowar NNPP cikin jam'iyyu na sahun gaba ya baiwa yan Najeriya sabon zabi baya ga APC da PDP.

Ku zabi APC don saka wa Buhari - Lawan

A wani labarin kuma Shugaban Majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya soki PDP bisa nuna rashin damuwa da arewa maso gabas a mulkinta

Ahmad Lawan ya roki mutanen arewa maso gabashin Najeriya da suka sakawa Buhari bisa alherin da ya masu ta hanyar sake zaben APC.

Lawan ya yi wannan jawabin ne a wurin ralin kamfen ɗan takarar shugaban kasa a inuwar APC, Bola Tinubu, wanda ya gudana a Bauchi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel