'Yan Najeriya Suna da Wani Zabin Bayan APC da PDP, Inji Kwankwaso

'Yan Najeriya Suna da Wani Zabin Bayan APC da PDP, Inji Kwankwaso

  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce yan Najeriya suna da wani zabin bayan APC da PDP sun gaza
  • Dan takarar shugaban kasa a inuwar NNPP mai kayan dadi ya ce Najeriya na fama da babban kalubale a bangaren ilimi
  • Tsohon gwamnan yace idan ya zama shugaban ƙasa zai rubanya nasarorin da ya samu a jihar Kano

Abuja - Ɗan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar New Nigeria Peoples Party, Rabiu Kwankwaso, yace idan ya ci zabe zai ruɓanya nasarorin da ya samu lokacin yana gwamnan Kano.

Kwankwaso ya faɗi haka ne a Abuja ranar Litinin a wurin zauren al'umma na masu neman zama shugaban kasa, wanda tsangayar koyar da kimiyyar siyasa na jami'ar Abuja ta shirya.

Sanata Kwankwaso.
'Yan Najeriya Suna da Wani Zabin Bayan APC da PDP, Inji Kwankwaso Hoto: @KwankwasoRM
Asali: Twitter

Tsohon gwamnan jihar Kano ya koka kan yadda Najeriya ke fuskantar rikice-rikice a ɓangaren ilimi tun daga matakin karatun Firamare zuwa manyan makarantu.

Kara karanta wannan

'Babban Abinda Atiku Abubakar Ya Rasa Wanda Ka Iya Jawo Masa Faɗuwa a Zaben 2023'

Ɗan takarar jam'iyya mai kayan maramari NNPP ya bayyana cewa manyan jam'iyyu APC da PDP sun gaza, sun kunyata 'yan Najeriya, kamar yadda jaridar Punch ta rahoto.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ina farin ciki da jin daɗi 'yan Najeriya suna da wani zabin bayan gazawar jam'iyyun APC da kuma PDP," Inji Kwankwaso.

A cewar Sanata Kwankwaso, batun Ilimi batu ne mai matukar muhimmanci kuma idan ya zama shugaban kasa, gwamnatinsa zata shawo kan matsalolin daki-daki.

A ruwayar Channels tv, Kwankwaso ya ci gaba da cewa:

"A kundin manufofinmu, mun ce da zaran ka tsallake ka samu makin da ake bukata a jrabawar JAMB, zaka yi amfani da ita tsawon shekaru huɗu."
"Bamu bukatar ka sake komawa ka zauna jarabawar saboda mun yi imani cewa tilas gwamnati ta ɗauki nauyin tabbatar da 'ya'yanta maza da mata talakawa sun samu damarmakin zuwa Jami'a kamar saura."

Kara karanta wannan

Gwamna Kuma Farfesa Ya Bayyana Mutum Ɗaya Tilo da Zai Iya Ceto Najeriya a 2023

"Don haka abinda muka fi amanna da shi ne ilimi, ilimi da ilimi."

Da yake jawabi, shugaban jami'ar UNIABUJA, Abdul-Rasheed Na’Allah, ya yi kira ga sauran masu neman kujerar shugaban kasa da su zo su gaya wa 'yan Najeriya dalilin da yasa suke neman mulki.

Ahmad Lawan Ya Bayyana Goyon Bayansa Ga Tinubu a Taron Bauchi

A wani labarin kuma Shugaban Majalisar dattawa ya caccaki PDP bisa nuna rashin damuwa da arewa maso gabas a mulkinta

Sanata Ahmad Lawan ya roki mutanen arewa maso gabashin Najeriya da suka sakawa Buhari bisa alherin da ya masu ta hanyar sake zaben APC

Lawan ya yi wannan jawabin ne a wurin ralin kamfen ɗan takarar shugaban kasa a inuwar APC, Bola Tinubu, wanda ya gudana a Bauchi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel